Trends

Bankin Duniya: Mutane Miliyan 139 a Najeriya Suna Cikin Mawuyacin Talauci

capital, business, finance, economy, banking and money concept 3D rendering animation.

Bankin Duniya ya bayyana damuwa cewa duk da kokarin da Najeriya ke yi wajen daidaita tattalin arzikinta, kimanin mutane miliyan 139 yanzu suna rayuwa cikin talauci. Bankin ya gargadi gwamnati cewa za a iya rasa nasarorin da aka samu idan ba a tabbatar da cewa gyare-gyaren tattalin arziki sun haifar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan kasa ba.

Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da rahoton Nigeria Development Update (NDU) na watan Oktoba 2025 mai taken “Daga Manufofi Zuwa Jama’a: Kai Amfanin Gyare-gyare Gida.”

Rahoton NDU, wanda ake fitarwa sau biyu a shekara, na duba halin tattalin arziki, manufofin gwamnati, da manyan kalubale da Najeriya ke fuskanta.

A jawabinsa — wanda shi ne karo na farko tun bayan hawansa ofis watanni uku da suka gabata — Verghis ya yabawa matakan gyare-gyaren gwamnati musamman wajen daidaita farashin musayar kudi da kuma soke tallafin man fetur, yana mai cewa wadannan su ne “ginshikan sauyi” da za su iya canza tsarin tattalin arzikin kasar nan na dogon lokaci.

“A cikin shekaru biyu da suka gabata, Najeriya ta dauki matakai masu karfi wajen gyaran tattalin arziki, musamman a bangaren musayar kudi da tallafin fetur. Wadannan su ne matakan farko da za su iya gina sabuwar tafarkin cigaban tattalin arziki,” in ji shi.

Ya kwatanta wannan dama da irin sauye-sauyen tarihi da aka gani a kasashen kamar Indiya a farkon shekarun 1990, yana mai jaddada cewa irin wannan dama kan zo sau daya ne, kuma dole ne a yi amfani da ita cikin hikima.

Verghis ya ce gyare-gyaren sun fara haifar da sakamako mai kyau: ci gaba na karuwa, kudaden shiga suna tashi, bashin kasa yana raguwa, kasuwar musayar kudi tana daidaituwa, ajiyar kudin kasa tana karuwa, kuma hauhawar farashi (inflation) tana raguwa sannu a hankali.

“Wadannan sakamakon suna nuna matakin daidaitawa na tattalin arziki. Wannan babbar nasara ce da kasashe da dama za su yi kishi da ita,” in ji shi.

Sai dai, ya jaddada cewa wadannan ci gaban a fannin tattalin arziki ba su kai ga inganta rayuwar talakawa ba.

“Duk da wadannan nasarori, gidaje da dama har yanzu suna fama da raguwar karfin saye. Talauci ya fara karuwa tun daga shekarar 2019 sakamakon wasu kura-kuran manufofi da tasirin annobar COVID-19, kuma har yanzu yana karuwa bayan gyare-gyare. A shekarar 2025, muna kiyasta cewa mutane miliyan 139 a Najeriya suna cikin talauci,” in ji shi.

Wannan adadi ya karu daga miliyan 129 da aka ruwaito a watan Afrilu 2025, da miliyan 87 a 2023, abin da ke nuna karuwar wahala a gidajen ‘yan kasa duk da cigaban tattalin arziki.

Bankin Duniya ya ce rahoton ya bayyana muhimman abubuwa uku da za su taimaka wajen fassara manufofi zuwa ci gaban rayuwar jama’a:

  1. Rage hauhawar farashi (inflation);
  2. Yin amfani da kudaden gwamnati ta hanya mai inganci;
  3. Faɗaɗa tsarin tallafin zamantakewa don kare talakawa da masu rauni.

Verghis ya ce ya zama dole a mayar da hankali kan farashin kayan abinci, saboda idan farashin ya ci gaba da tashi, zai iya rage goyon bayan jama’a ga gyare-gyaren gwamnati.

“Hauhawar farashin abinci na shafar kowa, musamman talakawa. Idan farashin abinci bai daidaita da na kasashen abokan hulɗar Najeriya ba, hakan zai kara matsa lamba a kan musayar kudi. Idan aka rage inflation, kudin ruwa (interest rate) zai sauka, kuma tattalin arziki zai habaka,” ya bayyana.

Ya yaba da manufofin Bankin CBN wajen tsauraran matakan tattalin arziki da kuma yadda gwamnati ke taka-tsantsan a fannin kasafin kudi, amma ya ce hakan bai isa ba wajen dakile hauhawar farashi cikin gaggawa.

Don haka, ya bukaci sauran gyare-gyaren tsari (structural reforms) domin magance matsalolin da ke cikin tsarin samar da abinci, rarrabawa da kasuwanci.

“Dole ne a hada manufofin kudi da kasafin gwamnati da gyare-gyaren tsari da nufin rage hauhawar farashin abinci wanda tushensa ya samo asali daga matsalolin samarwa da kasuwanni,” in ji shi.

Bankin Duniya ya kuma bukaci Najeriya ta inganta tsarin kula da kudaden jama’a (public financial management) domin tabbatar da cewa kowace naira da gwamnati ke kashewa na haifar da ainihin cigaban kasa, tare da faɗaɗa tsarin tallafin zamantakewa (social safety nets) don kare talakawa daga illar gyare-gyaren tattalin arziki.

Verghis ya jaddada cewa Bankin Duniya zai ci gaba da tallafawa Najeriya ta hanyar shawarwari, taimakon fasaha, da tallafin kudi, amma nasarar hakan za ta dogara da karfin siyasa da tattaunawa tsakanin gwamnati da jama’a.

“Kalubale ya bayyana: yadda za a fassara nasarorin gyare-gyare zuwa ingantacciyar rayuwa ga kowa. Wannan ba magana ce ta ka’ida kawai ba, amma aiki ne da zai iya juyar da daidaiton tattalin arziki zuwa kyakkyawar rayuwa,” in ji shi.

Taron NDU ya hada manyan jami’an gwamnati, shugabannin kamfanoni, abokan ci gaba, kungiyoyin farar hula, da ‘yan jarida don tattauna makomar tattalin arzikin Najeriya.

Bankin Duniya ya kammala da cewa duk da ci gaban da aka samu a fannin daidaiton tattalin arziki, nasarar dogon lokaci za ta dogara ne da yadda gyare-gyaren za su kai fa’ida ga talakawa.