Sanata Daga Enugu Ya Bar Jam’iyyar Labour Ya Shiga APC

Sanata Kelvin Chukwu da ke wakiltar Enugu ta Gabas

Sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas, Kelvin Chukwu, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Labour Party (LP) zuwa All Progressives Congress (APC). An karanta wasikar ficewarsa a zaman majalisar dattawa da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, ya jagoranta a ranar Laraba.

A cikin wasikar, Chukwu ya ce matakinsa ya biyo bayan tattaunawa da jama’arsa da sauran masu ruwa da tsaki a mazabarsa.

Chukwu na daga cikin ’yan majalisar tarayya 43 (sanatoci 8 da mambobin majalisar wakilai 35) da jam’iyyar LP ta fitar a zaben 2023. Sai dai wasu daga cikinsu sun riga sun bar jam’iyyar da ta ba su damar tsayawa takara.

A baya, sakataren yada labarai na kasa na LP, Obiora Ifoh, ya soki irin wannan mataki na ficewa daga jam’iyyar, yana mai cewa “mataki ne marar hujja kuma sabawa tsarin dimokuradiyya.”

Tun bayan kafa ta a 2002, jam’iyyar Labour Party ta taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, amma a zaben 2023 ne ta samu nasararta mafi girma — ta lashe kujerar gwamna, sanatoci 8, da wakilai 35, tare da samun dimbin kujeru a majalisun dokoki na jihohi.