Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya sauka daga mukaminsa, inda ya mika ragamar shugabancin hukumar ga May Agbamuche, wacce za ta rike mukamin shugabar riko na hukumar.
Agbamuche, wacce ita ce kwamishina mafi dadewar aiki a hukumar, za ta shugabanci INEC na ɗan lokaci har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban dindindin.
Farfesa Yakubu ya sanar da wannan sauyin shugabanci ne a ranar Talata, yayin wani taro da ya gudanar tare da kwamishinonin zabe na jihohi a ofishin babban birnin tarayya, Abuja.
Ya bukaci dukkan kwamishinoni da daraktoci na hukumar da su bai wa Agbamuche cikakken goyon baya a lokacin da take jagorantar hukumar, har sai an nada sabon shugaban hukumar gaba daya.







