Trends

Zaben Fidda Gwani: Jam’iyyar APC Ta Hana ‘Yan Takarar Majalisar Dattawa 47

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da hana ‘yan takarar Majalisar Dattawa guda 47 shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar gabanin babban zaben shekarar 2027.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Felix Morka, ya fitar a ranar Litinin a Abuja bayan kammala aikin tantance ‘yan takarar da kwamitocin tantancewa suka gudanar.

A cewar sanarwar, ‘yan takarar da abin ya shafa sun kasa samun sahalewa bisa ka’idoji da tanade-tanaden jam’iyyar APC na gudanar da zabukan fidda gwani.

Daga cikin fitattun mutanen da aka hana tsayawa takarar akwai tsohon Sanatan Bayelsa ta Gabas, Ben Murray-Bruce, tsohon mai neman takarar Majalisar Dattawa daga Babban Birnin Tarayya Abuja, Usman J. Wowo, da kuma dan siyasar jihar Rivers, Tamunobaabo Wemike Danagogo.

Sauran wadanda aka hana sahalewa sun fito daga jihohin Adamawa, Anambra, Cross River, Delta, Jigawa, Kebbi, Kwara, Nasarawa, Niger, Oyo, Plateau, Rivers, Taraba, Yobe da Zamfara.

A yankin Adamawa ta Arewa, APC ba ta sahale Hon. Hamish Idris da Hon. Abdurman Kwacham ba. Haka kuma a Bayelsa ta Gabas, an hana Ben Murray-Bruce da Sanata Benson Agadaga shiga takarar.

A jihar Oyo kuwa, jam’iyyar ta hana Ademola Wasiu Alli, Ajimobi Wasiu Adegboyega, Kolapoboye Kola Daisi da Akinremi Alade Bolaji shiga zaben fidda gwani.

A jihar Rivers ma, daga cikin wadanda ba su samu sahalewa ba akwai Oyukaye Flag Amachree, Tamunobaabo Wemike Danagogo, Jack-Rich Tein da Banigo Ipalibo.

Jihar Zamfara ce ta fi kowace jiha yawan wadanda aka hana tsayawa takara, inda ‘yan takara bakwai daga mazabun Sanatan Tsakiya, Arewa da Yamma suka gaza samun sahalewa.

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa an gudanar da aikin tantancewar ne bisa dokoki da ka’idojinta na cikin gida, amma ba ta bayyana takamaiman dalilan da suka sa aka hana wadannan ‘yan takarar shiga zaben fidda gwani ba.

Ana sa ran APC za ta ci gaba da gudanar da zabukan fidda gwani na sanatoci a wani bangare na shirye-shiryenta na babban zaben shekarar 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *