Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi jami’anta da su guji amfani da kafafen sada zumunta, tana mai cewa duk wani soja da ya karya dokokin kasar kan amfani da kafafen sada zumunta zai fuskanci hukunci.
Babban Provost Marshal na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Mathias Erebulu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron horaswa ga jami’an ‘yan sandan soja, wanda gidan talabijin na African Independent Television (AIT) ya ruwaito a ranar Alhamis.
Erebulu ya umarci kwamandoji da shugabannin rundunoni da su koma sansanoninsu domin wayar da kan sojoji kan illolin amfani da kafafen sada zumunta ba bisa ka’ida ba.
“Sojojinmu ba su da wani aiki a kafafen sada zumunta. Duk lokacin da suka karya dokar farko ta kafafen sada zumunta, ana hukunta su.
“Saboda haka ya zama wajibi ga kwamandoji da shugabannin rundunoni su koma yankunansu su sake jaddada illolin da ke tattare da amfani da kafafen sada zumunta ba daidai ba,” in ji shi.
Janar din ya kuma tunatar da jami’an soja iyakar ikon da kundin tsarin mulkin kasa ya ba su wajen tsare fararen hula a wuraren sojoji. Ya ce duk wani farar hula da sojoji suka kama dole ne a mika shi ga hukumar da ta dace cikin sa’o’i 24 bayan gudanar da binciken farko.
“Bisa kundin tsarin mulki, ba a yarda mu rika tsare fararen hula a wurarenmu ba.
“Saboda haka ana tunatar da su cewa duk lokacin da aka kama wani farar hula, bayan gudanar da binciken da ya dace, cikin sa’o’i 24 dole ne a mika shi ga hukumar da ke da alhakin kula da irin wannan batu,” in ji Erebulu.
Taron horaswar, wanda ya mayar da hankali kan da’a da bin ka’ida a aikin jami’an ‘yan sandan soja, an nuna shi ne a shirin safiya na gidan talabijin na AIT mai suna Kakaaki.






