Dangote Na Shirin Saka Hannun Jarin Kamfanin Siminti a Kasuwar London

Aliko Dangote na nazarin yiwuwar saka wani kaso na kamfanin Dangote Cement Plc a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta London domin fadada hanyoyin samun jari daga manyan masu zuba hannun jari na duniya.

Rahoton da jaridar Financial Times ta wallafa ya ce shirin zai taimaka wajen kara darajar kamfanin, fadada masu zuba jari fiye da nahiyar Afirka, da kuma karfafa martabar kamfanin a kasuwannin duniya.

Kamfanin simintin na da karfin samar da tan miliyan 55 a shekara a kasashe sama da goma, lamarin da ya sanya shi cikin manyan kamfanonin siminti a Afirka. Ana sa ran cewa shiga kasuwar London zai taimaka wa kamfanin wajen samun karin kudade domin ci gaba da fadada ayyukansa a nahiyar.

Dangote Cement Plc na gudanar da manyan masana’antu a Nigeria, Ethiopia, Senegal, Tanzania da Zambia, yayin da kimar kasuwarsa ke tsakanin dala biliyan 10 zuwa 11.

Masana harkokin tattalin arziki sun bayyana cewa wannan mataki zai kara bai wa kamfanin damar samun jari mai dorewa daga kasashen waje domin tallafa wa manyan ayyukansa.

Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da Dangote Group ke ci gaba da fadada harkokinsa a bangarorin makamashi, taki da masana’antu. A watan Afrilu, Dangote Fertiliser Limited ta tara dala miliyan 750 ta hanyar sayar da takardun bashi masu zaman kansu, wanda ya zama daya daga cikin manyan mu’amalolin kamfanin a kasuwannin duniya.

Har ila yau, rukunin kamfanonin na shirin sayar da kusan kaso 10 cikin 100 na matatar mai ta dala biliyan 20 ta hanyar IPO a kasuwannin hannayen jari na Afirka, tare da duba yiwuwar fitar da wasu takardun bashi domin tallafa wa sababbin ayyuka.

Shirin fadada ayyukan Aliko Dangote ya hada da gina babbar tashar jiragen ruwa mafi girma a Najeriya, kara samar da takin urea, bunkasa harkokin gas, da kuma samar da tashar wutar lantarki mai karfin megawatt 20,000. Ana hasashen cewa jarin da za a zuba a waɗannan ayyuka zai kai dala biliyan 40 cikin shekaru biyar masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *