Gwamnatin Tarayya ta hannun Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA) ta bai wa kamfanonin dillalan man fetur guda shida lasisin shigo da tan 720,000 na Premium Motor Spirit (PMS), wato fetur.
Kamfanonin da aka bai wa lasisin sun hada da NIPCO Plc, AA Rano Nigeria Limited, Matrix Energy Group, Shafa Energy, Pinnacle Oil and Gas Limited da Bono Energy.
Matakin na zuwa ne duk da ikirarin da NMDPRA ta yi cewa matatar Dangote Petroleum Refinery yanzu tana samar da sama da kashi 90 cikin 100 na bukatar fetur ta yau da kullum a Najeriya.
Wani jami’in NMDPRA da ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana a hukumance, ya tabbatar wa wakilinmu cewa an bayar da lasisin shigo da man.
Bincike ya nuna cewa NIPCO Plc za ta shigo da tan 120,000, AA Rano Nigeria Limited tan 150,000, Matrix Energy Group tan 150,000, Shafa Energy tan 120,000, Pinnacle Oil and Gas Limited tan 120,000, yayin da Bono Energy za ta shigo da tan 60,000, wanda jimillarsu ta kai tan 720,000.
Sabbin amincewar na zuwa ne duk da cewa NMDPRA ta taba bayyana cewa babu bukatar ci gaba da shigo da fetur saboda Najeriya na da isasshen karfin tace mai a cikin gida bayan fara aiki da matatar Dangote.
Hukumar ta ce ba ta bayar da ko lasisi daya na shigo da fetur ba a zangon farko na shekarar 2026 saboda matatar Dangote na iya biyan bukatar kasar gaba daya.
Sai dai wani babban jami’in NMDPRA ya bayyana a ranar Alhamis cewa hukumar ba ta taba hana shigo da fetur ba, yana mai cewa tabbatar da wadatar makamashi shi ne babban abin da suke bai wa muhimmanci.
Ya ce hadin man da ake tacewa a cikin gida da wanda ake shigowa da shi daga waje ne zai tabbatar da daidaiton wadatar fetur a fadin kasar.
“Ba a taba sanya dokar hana shigo da fetur ba. Matsayar hukumar tun farko ita ce tabbatar da tsaron makamashi ga kasa. Burinmu shi ne tabbatar da cewa babu gibi wajen wadatar mai. Don haka, hada man cikin gida da wanda ake shigowa da shi daga waje zai tabbatar da dorewar wadatar mai,” in ji jami’in.
Ana iya tunawa cewa a watan Maris, tsohon shugaban NMDPRA, Saidu Mohammed, ya bayyana cewa hukumar ba ta kara shigo da fetur zuwa Najeriya. Ya gargadi masu kokarin mayar da kasar zamanin dogaro da shigo da fetur daga kasashen waje, yana mai cewa dole ne a kare nasarorin da aka samu a bangaren tace mai a cikin gida.
Ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin wata tawaga a hedikwatar hukumar da ke Abuja domin karfafa hadin gwiwa tsakanin kafafen yada labarai da hukumomin makamashi.
A cewarsa, har yanzu akwai wasu masu ruwa da tsaki da ke son a ci gaba da dogaro da shigo da fetur duk da ci gaban da aka samu a bangaren tace mai na cikin gida.
“Yanzu muna da matatar da za ta iya biyan bukatunmu. Amma har yanzu akwai wadanda ke sonmu ci gaba da zamanin shigo da fetur. Dole ne mu tabbatar da cewa an dore da nasarorin da aka samu,” in ji Saidu Mohammed.
Ya kara da cewa bangaren man fetur na Najeriya ya taba shiga matakai daban-daban, daga lokacin da kasar ke tace mai a cikin gida zuwa lokacin da aka dogara sosai da shigo da fetur bayan durkushewar matatun gwamnati.
A cewarsa, fiye da tankokin ajiye mai 200 ne suka bazu a gabar tekun Najeriya saboda yawan bukatar shigo da fetur a lokacin.
Sai dai shugaban Dangote Group, Aliko Dangote, ya musanta ikirarin cewa an daina bayar da lasisin shigo da fetur, yana mai cewa har yanzu ana ci gaba da bai wa kamfanoni irin wannan lasisi.
Majiyoyi daga matatar Dangote sun bayyana cewa kamfanin na iya ƙarkata gaba ɗaya zuwa fitar da kayayyakin man da yake tacewa zuwa kasashen waje idan gwamnatin tarayya ta ci gaba da bayar da lasisin shigo da fetur.
Wani babban jami’i a kamfanin Dangote ya ce matatar na iya fitar da dukkan kayayyakin da take samarwa idan aka ci gaba da bai wa masu shigo da fetur lasisi.
“Tun da har yanzu ana bayar da lasisin shigo da fetur, mu ma za mu iya mayar da hankali wajen fitar da duk abin da muke samar wa zuwa kasashen waje,” in ji jami’in da ya nemi a sakaya sunansa.
Lokacin da aka tambaye shi ko hakan ba zai iya haddasa karancin mai a Najeriya ba, jami’in ya ce ya kamata gwamnati ta kare masana’antun cikin gida musamman a lokacin da ake fama da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ya ce shugaban Donald Trump na kokarin kare masana’antun Amurka, yayin da sauran kasashe su ma ke kare nasu kasuwanni.
“Idan sun san za a iya samun ƙarancin mai, me ya sa suke bayar da lasisin shigo da fetur alhali duniya na ƙoƙarin kare masana’antunta? Donald Trump na kare Amurka, sauran kasashe ma suna kare nasu masana’antu. Najeriya ba za ta iya jure wani sabon karancin makamashi ba, musamman a daidai lokacin da ake fargabar karancin mai a duniya saboda yaki,” in ji majiyar.






