Taiwo Oyedele ya bayyana cewa Najeriya ta samu ci gaban Gross Domestic Product (GDP) na kashi 11.2 cikin 100 a ma’aunin dalar Amurka a shekarar 2025, lamarin da ke kara karfafa burin kasar na gina tattalin arzikin da zai kai dala tiriliyan daya nan da shekarar 2030.
Yayin wata ganawa da masu zuba jari na duniya a Paris, Oyedele ya ce wannan ci gaban na nuna karuwar amincewar masu zuba jari da kuma tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa.
A cewarsa, gwamnatin na ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da manufofin tattalin arziki masu dogaro da tsarin kasuwa tare da tabbatar da daidaiton harkokin kudi na dogon lokaci domin jawo karin jari da bunkasa tattalin arziki.
“Ba za mu dawo da tallafin mai ba saboda yana haifar da matsaloli ga tattalin arziki, sannan ba za mu kafa tsarin kayyade farashi ba saboda mun yi imani da tsarin kasuwa,” in ji shi.
Taiwo Oyedele ya kuma bayyana cewa rikice-rikicen siyasa da ake fama da su a Iran na iya samar wa Najeriya sabbin damammaki yayin da kasashen duniya da masu zuba jari ke neman sababbin hanyoyin samar da makamashi da sabbin kasuwanni.
“Halin da ake ciki a Iran na samar mana da sababbin damammaki yayin da duniya ke kokarin fadada hanyoyin samar da makamashi da zuba jari a sababbin kasuwanni,” ya kara da cewa.
Ministan ya ce ajandar gyaran tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali ne wajen gina tattalin arziki mai karfin gasa ta hanyar tsauraran matakan kula da harkokin kudi, manufofi masu jan hankalin masu zuba jari, da kuma bunkasa tattalin arziki karkashin jagorancin bangaren masu zaman kansu.
Wadannan kalamai na zuwa ne yayin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a bangaren tattalin arziki, ciki har da cire tallafin mai, gyaran tsarin haraji, da sassauta tsarin musayar kudaden kasashen waje domin farfado da tattalin arzikin kasa mafi girma a nahiyar Afirka.






