Masana harkokin lafiya sun yi gargadi kan karuwar masu fama da gazawar koda a Najeriya, suna danganta matsalar da jinkirin zuwa asibiti da kuma rashin bin shawarwarin magani yadda ya kamata.
Tsohon shugaban Nigerian Association of Nephrology, Jacob Awobusuyi, ya bayyana cewa mutane da dama da aka gano suna dauke da cutar koda ba sa ci gaba da jinya ko dawowa domin duba lafiyarsu bayan fara magani.
“A lokacin da yawanci suke zuwa wurinmu, kodar ta riga ta fara gazawa ko kuma cutar ta kai wani mataki mai hadari,” in ji shi.
Jacob Awobusuyi ya jaddada cewa gano cutar da wuri na iya rage saurin lalacewar koda tare da kara yiwuwar rayuwar marasa lafiya.
“Idan aka gano cutar da wuri, akwai hanyoyi da dama da za mu bi domin rage saurin lalacewar aikin koda,” ya bayyana.
Ya ce amfani da magunguna, bin tsarin rayuwa mai kyau da kuma yin gwaje-gwaje akai-akai na iya taimakawa wajen jinkirta tabarbarewar cutar, amma marasa lafiya da dama kan daina zuwa jinya bayan an fara gano cutar.
Likitan ya danganta wannan matsala da karancin wayar da kan jama’a game da lafiya, inda mutane da yawa ke amfani da magungunan gargajiya ko yin maganin kansu kafin neman kulawar likitoci.
“Mutane da yawa suna amfani da hadin ganyayyaki ko magungunan da ba a tantance su ba kafin zuwa asibiti,” in ji shi.
Kididdigar Nigerian Association of Nephrology ta nuna cewa sama da mutum miliyan 20 a Najeriya na dauke da cutar koda, yayin da kusan mutum 20,000 ke shiga matsanancin hali na gazawar koda duk shekara, wanda ke bukatar wankin koda ko dashen koda.
Gazawar koda, wadda ake kira end-stage renal disease, cuta ce da ba ta warkewa gaba daya, amma ana iya sarrafa ta ta hanyar wankin koda ko dashen koda. Manyan abubuwan da ke haddasa cutar sun hada da hawan jini, ciwon sukari, kumburin koda, da kuma yawaitar amfani da magungunan rage radadi ba tare da kulawar likita ba.
Jacob Awobusuyi ya kara da cewa duk da cewa karuwar yawan masu fama da cutar na iya kasancewa sakamakon karin gwaje-gwajen gano cutar, jinkirin zuwa asibiti har yanzu na daga cikin manyan matsalolin da ke hana samun nasarar magani.






