Gwamnati Za Ta Fadada Horaswa da Samar da Ayyukan Yi Ga Ungozoma

Gwamnatin Tarayya ta bayyana sabbin shirye-shirye domin karfafa aikin ungozoma tare da inganta lafiyar mata masu juna biyu da jarirai a fadin Najeriya.

Da yake jawabi yayin bikin ranar International Day of the Midwife na shekarar 2026 a Abuja, Ministan Lafiya da Jin Dadin Jama’a na Tarayya, Muhammad Ali Pate, wanda Abisola Adegoke ta wakilta, ya ce ungozoma su ne ginshikin kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai musamman a yankunan karkara da ba su da isassun kayan kiwon lafiya.

Ya ce, “Babu wani tsarin lafiya da zai iya samar da ingantaccen kulawa ga mata da yara ba tare da kwararrun ungozoma masu yawa ba. Su ne ke kare rayuka tun daga daukar ciki har zuwa haihuwa da bayan haihuwa.”

Ma’aikatar Lafiya ta kuma kaddamar da shirin Nigeria Strategic Directions for Nursing and Midwifery 2025–2030, wanda aka tsara domin kara yawan ma’aikatan jinya da ungozoma, sabunta tsarin koyarwa, da kuma inganta jagoranci da ayyukan kula da lafiya.

Shirin ya hada da fadada cibiyoyin horas da ma’aikatan jinya da ungozoma, kara yawan daliban da ake dauka, samar da ayyukan yi, da kuma tabbatar da rarraba ungozoma yadda ya kamata zuwa yankunan karkara.

Har ila yau, shirin ya ba da fifiko ga ci gaba da horas da ma’aikata ta hanyar koyar da dabaru masu inganci da kwarewar ceton rayuka.

Muhammad Ali Pate ya kuma bayyana shirin Maternal Mortality Reduction Innovation Initiative (MAMII), wanda aka kirkira domin rage mace-macen mata masu juna biyu da masu haihuwa a yankunan da matsalar ta fi kamari.

Ya ce manufar shirin ita ce tabbatar da cewa “babu wata mace da za ta mutu yayin haihuwa.”

Ministan ya jaddada cewa gwamnati na kokarin cire duk wani cikas ga daukar ma’aikatan ungozoma aiki, tabbatar da rarraba su cikin adalci a fadin kasar, da kuma daidaita tsarin koyarwa da ka’idojin duniya.

Ma’aikatar ta sake tabbatar da cewa wadannan sauye-sauyen za su taimaka wajen inganta lafiyar mata masu juna biyu da jarirai tare da mayar da ungozoma a matsayin muhimmin bangare na sauya fasalin harkar lafiya a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *