Bello El-Rufai da Wasu ‘yan Majalisa Hudu sun Sauya Sheka a Wani Sauyin Siyasa

Sabbin sauya shekar jam’iyya sun sake girgiza Majalisar Wakilai ta Tarayya, inda ‘yan majalisa biyar suka fice daga jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) zuwa Nigeria Democratic Congress (NDC) da African Democratic Congress (ADC) gabanin babban zaben shekarar 2027.

Daga cikin wadanda suka sauya shekar akwai Muhammed El-Rufai, dan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kuma mai wakiltar mazabar Kaduna North a Majalisar Wakilai. Muhammed El-Rufai ya sanar da ficewarsa daga APC zuwa NDC a hukumance yayin zaman majalisar na ranar Alhamis. Masu lura da al’amuran siyasa na ganin matakin na kara nuna yadda sabanin siyasa ke kara tsananta tsakanin bangaren siyasar El-Rufai da jam’iyyar APC mai mulki.

Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta takardun sauya shekar a zauren majalisar. Ficewar Muhammed El-Rufai na zuwa ne bayan watanni ana rade-radin makomarsa ta siyasa, musamman bayan mahaifinsa Nasir El-Rufai ya rika sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Tsohon gwamnan Kaduna, wanda a baya ake kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan makusantan Tinubu a APC, ya zargi jam’iyyar da yin watsi da dimokuradiyya cikin gida tare da ware masu biyayya da ruwa a jallo.

Haka kuma Joshua Obika, mai wakiltar mazabun Abaji/Gwagwalada/Kuje/Kwali a Babban Birnin Tarayya (FCT), ya koma NDC daga APC. Wannan shi ne karo na uku da Obika ke sauya jam’iyya tun bayan rantsar da majalisa ta 10.

An zabe shi ne a karkashin jam’iyyar Labour Party a shekarar 2023 kafin daga bisani ya koma APC a watan Maris na 2026.

Shi ma Abdulhakeem Kamilu, mai wakiltar mazabar Wudil/Garko ta jihar Kano, ya fice daga ADC zuwa NDC, inda ya danganta matakin da rikicin shugabanci da ya ce ya ki ci ya ki cinyewa a jam’iyyar.

Kamilu ya shiga majalisar ne a karkashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) kafin daga bisani ya koma ADC.

A wani bangare kuma, ‘yan majalisar Kaduna biyu — Suleiman Richifa da Umar Ajilo — sun fice daga PDP zuwa ADC.

‘Yan majalisar sun bayyana cewa rikice-rikicen da suka dabaibaye PDP a matakin jiha da na kasa ne suka tilasta musu daukar matakin.

Sabuwar guguwar sauya shekar na zuwa ne kwanaki kadan bayan rahotannin cewa akalla ‘yan majalisa 17 sun bayyana goyon bayansu ga NDC, lamarin da ke nuna yadda ake ci gaba da sake fasalin kawancen adawa gabanin zaben 2027.

Wannan ci gaban ya sake sauya daidaiton siyasa a Majalisar Wakilai tare da kara hasashen cewa karin sauya shekar na iya biyo baya a watanni masu zuwa yayin da tuntuba da tattaunawar hadaka ke ci gaba tsakanin manyan bangarorin siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *