Trends

Shugaba Tinubu Zai Karɓi Ƙungiyar Super Falcons a Fadar Aso Villa

Yan wasan Super Falcons

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya karɓar Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Mata ta Ƙasa, wato Super Falcons, a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Super Falcons sun doke Ƙungiyar Mata ta Ƙasar Morocco, Atlas Lionesses, a wasan ƙarshe na WAFCON da aka buga a karshen mako, inda suka fito da nasara mai kayatarwa.

Ziyarar Ƙungiyar zuwa fadar Shugaban Ƙasa na daga cikin jerin bukukuwa da tarukan girmamawa da aka tsara domin karrama matan kwallon ƙafa bisa namijin kokarinsu da suka sake baiwa Najeriya suna a matakin nahiyar Afirka.

Nasarar da Falcons suka samu ta haddasa murna da shagulgula a fadin kasar, inda masoya wasanni da manyan ‘yan siyasa ke ta yaba wa jajircewa, bajinta da kwarewar ‘yan wasan.

Taron karɓar su a fadar shugaban ƙasa zai kuma jaddada kudirin gwamnatin Tinubu wajen habaka harkar wasanni da kuma tallafa wa ‘yan wasa na Najeriya a matakai daban-daban.