Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya sanar da korar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, daga jam’iyyar, tare da hana shi hulɗa da jam’iyyar har na tsawon shekaru 30 masu zuwa.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Araba Aiyenigba, ya fitar, inda ya bayyana cewa El-Rufai ya yi ƙarya game da kasancewarsa ɗan jam’iyyar, ya yi katsalandan a cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar, tare da ƙoƙarin rushe tsarin jam’iyyar ta hanyoyi marasa doka da dabarun siyasa masu ruɗani.
Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa ya yanke wannan hukunci ne bayan gudanar da cikakken bincike kan ikirarin El-Rufai na shiga jam’iyyar, wanda aka ce ya janyo rudani da rikice-rikice da kuma barazana ga haɗin kai da akidar jam’iyyar.
Sanarwar ta bayyana cewa El-Rufai bai yi rijista a mazabarsa ta asali ba kamar yadda kundin tsarin mulkin SDP ya tanada. Amma duk da haka, ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa ya shiga jam’iyyar. Har ila yau, an zarge shi da ƙirkirar takardu da kuma daukar hoto da wasu shugabannin jam’iyyar da aka dakatar, domin ƙarfafa ƙaryar da ya faɗa.
Jam’iyyar ta bayyana cewa da fari sun ba shi dama saboda matsayin da ya taɓa rike a gwamnati, amma binciken da aka gudanar daga baya ya tabbatar da cewa bai shiga jam’iyyar SDP ba. A cewar SDP, maimakon goyon bayan jam’iyyar, El-Rufai yana tallata wasu jam’iyyun siyasa daban.
Bugu da ƙari, SDP ta zargi El-Rufai da haɗin guiwa da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) tare da ƙoƙarin jawo SDP cikin wata haɗakar siyasa da ba ta da amincewa daga jam’iyyar.
Saboda haka, jam’iyyar ta ce da zarar an tabbatar da bayyana El-Rufai a fili a matsayin mamba na ADC, ba ta da wani zaɓi illa yanke duk wata alaƙa da shi. Daga yanzu, an haramta masa amfani da sunan jam’iyyar, alamar jam’iyyar, ko shiga duk wani abu da ya shafi jam’iyyar na tsawon shekaru 30, daga yau zuwa nan gaba.
SDP ta bukaci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da sauran hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cewa El-Rufai ba ɗan jam’iyyar bane kuma ba shi da izinin wakiltar jam’iyyar a kowanne mataki.
Jam’iyyar ta jaddada ƙudurinta na ci gaba da bin tsarin dimokuraɗiyya da siyasar da ke kan gaskiya da doka, tana kuma ƙarfafa wa duk ‘yan Najeriya da ke sha’awar shiga jam’iyyar da su bi matakan doka.
Abin sha’awa, El-Rufai kwanan nan ya nuna niyyar gudanar da bikin maraba da shi a ofishin jam’iyyar na ƙasa a Abuja, sai dai an tunatar da shi da ya fara yin rajista a mazabarsa ta Jihar Kaduna. Amma maimakon bin tsarin doka, sai ya ƙirkiri takardun da ke nuna shi ne mamba na farko a mazabar, lamarin da ya ci karo da dukkan bayanan jam’iyyar.
Wannan rikicin ya biyo bayan murabus da El-Rufai ya yi daga jam’iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC), inda ya bayyana cewa akwai sabani tsakanin akidunsa da salon tafiyar jam’iyyar APC a yanzu.

7h3wtk