Trends

Afirka Na Dauke da Kashi 68% na Sabbin Masu Cutar Hepatitis B — WHO

Wani sabon rahoto daga World Health Organization (WHO) ya nuna cewa duk da ci gaban da ake samu wajen yaki da cutar hepatitis, har yanzu cutar na ci gaba da kasancewa babbar barazana ga lafiyar al’umma a duniya.

Rahoton ya bayyana cewa a shekarar 2024, cutukan hepatitis B da C sun yi sanadin mutuwar mutum miliyan 1.34 a duniya, yayin da sama da mutum 4,900 ke kamuwa da sabbin cututtukan a kowace rana. WHO ta kiyasta cewa mutum miliyan 287 ne ke rayuwa da cutar hepatitis B ko C mai dorewa a shekarar.

Kasashe goma da suka hada da Nigeria, China, India, Indonesia, South Africa, Ghana, Ethiopia, Bangladesh, Philippines da Vietnam ne suka dauki kashi 69 cikin 100 na mace-macen da cutar hepatitis B ta haddasa.

Dangane da hepatitis C, rahoton ya ce matsalar ta fi bazuwa a kasashe daban-daban, inda Nigeria ke cikin kasashe goma da suka dauki kashi 58 cikin 100 na mace-macen da cutar ke haddasawa a duniya.

Duk da girman matsalar, rahoton ya nuna cewa yawan masu samun magani har yanzu bai kai yadda ake bukata ba. Kasa da kashi 5 cikin 100 na masu hepatitis B ne suka samu magani a shekarar 2024, yayin da kashi 20 cikin 100 kawai na masu hepatitis C suka taba samun magani tun bayan samuwar magungunan warkarwa a shekarar 2015.

WHO ta ce mutum miliyan 1.1 sun mutu sakamakon hepatitis B, yayin da mutum 240,000 suka mutu saboda hepatitis C a shekarar 2024. Rahoton ya bayyana cewa lalacewar hanta da cutar kansar hanta na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa mace-macen.

Rahoton ya kuma nuna cewa yankin Afirka ne ya dauki kashi 68 cikin 100 na sabbin masu kamuwa da hepatitis B, amma kashi 17 cikin 100 kacal na jariran da aka haifa ne suka samu allurar rigakafin farko bayan haihuwa.

Rahoton ya yaba wa kasashe irin su Egypt, Georgia, Rwanda da United Kingdom bisa nasarorin da suka samu, yana mai cewa hakan na nuna yiwuwar kawar da cutar gaba daya.

Tun daga shekarar 2015, sabbin masu kamuwa da hepatitis B sun ragu da kashi 32 cikin 100, yayin da mace-macen hepatitis C suka ragu da kashi 12 cikin 100 a duniya.

Babban Daraktan WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi gargadin cewa ci gaban da ake samu yana tafiya a hankali kuma ba daidai ba ne a ko’ina.

“Mutane da dama har yanzu ba a gano suna dauke da cutar ba kuma ba sa samun magani saboda wariya, raunin tsarin lafiya, da rashin samun kulawa cikin adalci,” in ji shi.

WHO ta yi kira ga kasashe da su kara yawan alluran rigakafi, fadada shirye-shiryen rage hadarin kamuwa da cutar, hana yada cutar daga uwa zuwa jariri, da kuma kara bai wa mutane damar samun magani, tana mai jaddada cewa hanyoyin kawar da hepatitis a matsayin barazana ga lafiyar jama’a nan da shekarar 2030 sun riga sun wanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *