Trends

Zaben 2027: Tinubu ba Zai Sami Kuri’un Arewacin Najeriya ba – In ji a Babachir Lawan

Babachir Lawan

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir David Lawal, ya bayyana cewa Arewacin Najeriya zai kada ƙuri’arsa ya fitar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027, saboda halin ƙuncin rayuwa da kuma manufofin gwamnati da ya ce sun ware yankin daga tsarin mulki da ci gaban ƙasa.

A wata hira da ya yi a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Trust TV, Babachir Lawal ya ce gwamnatin Tinubu ta kasa inganta rayuwar ‘yan Najeriya, kuma wasu fitattun shugabannin siyasa daga Arewacin ƙasar na shirin haɗa kai domin fitar da wani ɗan takara daban a 2027.

Ya ce: “Manufofi irin su cire tallafin man fetur da tsadar rayuwa sun ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin wahala. Duk wata gwamnati da ba ta kawo sauƙi ba, sai ta ƙara wahala – dole a dakatar da ita.”

Babachir ya ƙaryata cewa nadin mukamai da Tinubu ke yi kwanan nan don jan hankalin Arewacin Najeriya ne, yana mai cewa hakan “na’ura ce kawai ta kawar da hankali.”

Ya ce: “Wannan duk kwalliya ce ba ta biya kuɗin sabulu ba. Ni ne na fi fafutukar ƙin tikitin Musulmi-Musulmi. Idan na ga ya naɗa shugaban jam’iyyar APC Kirista, na fahimci Bola na shirin sake tikitin Musulmi-Musulmi.”

Lawal ya kara da cewa yawancin nade-naden da ake yi suna da manufa ta siyasa wadda ke nufin raba ƙuri’u da haifar da rigingimu a cikin al’umma. “Musulman da suka zaɓe shi, ya watsar da su, ya kunyata su, ya kuma hana yankin ci gaba,” in ji shi.

Ya tabbatar da cewa ƙungiyarsu ta Northern Political Consultative Group na aiki tare da Arewa Consultative Forum (ACF), Northern Elders Forum (NEF) da sauran ƙungiyoyin Arewacin Najeriya domin haɗa ƙarfi da ƙarfi gabanin 2027.

“Ni mamba ne na Arewa Consultative Forum. Muna kuma aiki tare da Northern Elders Forum da wasu. Muna cike gibi da juna. Ba za ka iya samun mulki ba sai ka haɗa kai da wata jam’iyya,” ya bayyana.

A matsayin sa na babban manomi, Lawal ya soki yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da harkar noma da batun samar da abinci.

“A bara, za mu sayar da buhun masara Naira 110,000, amma takin zamani Naira 45,000 ne. Yanzu takin zamani ya tashi zuwa Naira 70,000, amma masara ta fadi zuwa Naira 65,000. Sun shigo da masara da shinkafa da suka lalace daga waje, sun cika kasuwa da su, suka lalata amfanin manoma. Noma ya zama aikin da ba ya da amfani,” in ji Babachir.

Lawal ya jaddada cewa matakin da gwamnatin Tinubu ke dauka ba ya amfani da Arewa, kuma cewa an gama shirya tunkarar gwamnatin a zaɓe mai zuwa.

One thought on “Zaben 2027: Tinubu ba Zai Sami Kuri’un Arewacin Najeriya ba – In ji a Babachir Lawan

Comments are closed.