Trends

An Maida Maciji da Sauran Dabbobin da Aka Samu a Gidan Tsohon Akanta Janar Zuwa Gidan Zoo

Idris Ahmed Tsohon Akanta Janar

Shugaban Gidan Zoo na Kano, Malam Sadik Kura Muhammad, ya tabbatar da cewa an kama maciji (python) da ya tsere daga gidan tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, kuma an kwashe shi tare da wasu dabbobin jeji zuwa gidan Zoo na Kano.

Tserewar macijin ta jefa al’umma cikin tsoro da firgici a unguwannin Daneji da kewaye a Jihar Kano. Wasu daga cikin dabbobin da aka samu a gidan sun haɗa da kada (crocodile) da kuma ɗan damisa (cub).

Mazauna unguwannin dake makwabtaka da gidan — Daneji, Mandawari, Kabara, da Soron Dinki — sun bayyana cewa basu samu damar yin barci cikin kwanciyar hankali ba har sai da aka kama macijin aka kwashe shi daga yankin.

A wata hira da ya yi da gidan rediyo na cikin gida a Kano, Daraktan Zoo ya bayyana cewa saboda irin firgicin da lamarin ya haifar, tsohon Akanta Janar ɗin ya yanke shawarar miƙa dabbobin ga gwamnati da kansa, kuma yanzu suna cikin kulawar gidan Zoo.

Malam Muhammad ya ƙara da cewa Ahmed Idris yana da lasisi na mallakar dabbobin, kuma dabbobin ba su kai matakin da za su zama barazana ga jama’a ba.

Ya ce: “Akwai wata doka da ake kira Dokar Dabbobin Jeji, wadda ke baiwa mutum damar mallakar wasu nau’in dabbobi a gida. Wannan na iya haɗawa da nau’ukan da ke cikin haɗarin karewa da kuma waɗanda ba su da wannan barazanar.”

“Amma dabbobin da ke cikin haɗarin bacewa kamar tsuntsayen parrots da vultures, dole sai an ajiye su ne a gidan zoo domin kiyaye nau’insu da kuma habaka jinsinsu, ba domin nishaɗi ko sha’awa ba.”

Ya kuma bayyana cewa dokar ta tanadi buƙatun lasisi, samar da muhalli da ya dace, da kuma ciyarwa da tsaron dabbobin kafin a bayar da amincewa.

“Na tabbatar cewa yana da lasisi, kuma damisar da ke wurin ƙarami ce, ba ta da haɗari. Amma idan dabbobin sun kai wani girma, dole ne a miƙa su zuwa gidan zoo.”

“Saboda haka, lasisin na bukatar a sabunta shi a kowace shekara don tabbatar da cewa dabbobin ba su zama barazana ga kowa ba. Kafin kowace dabba ta zama barazana, ya kamata ta riga ta shiga hannun gwamnati.”

“Na ziyarci gidan, na tabbatar da cewa dabbobin ba su kai matakin da za su yi illa ba. Amma saboda koke-koken da maƙwabta suka yi, tsohon Akanta Janar ya yanke shawarar miƙa su da kansa. Mun je da dare muka kwashe su, yanzu suna cikin aminci a gidan zoo na Kano.”

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, shima ya tabbatar da cewa an fara bincike kan lamarin, kuma an gayyaci Ahmed Idris domin bayyana wasu abubuwa da suka shafi batun.