Trends

Shiga Jami’a: Lissafi Bai Zama Dole ga Masu Neman Karutun Fasaha – Gwamnatin Tarayya

Ministan Ilimi Dr. Tunji Alausa

Gwamnatin Tarayya ta amince da sabbin gyare-gyare a tsarin karɓar ɗalibai zuwa jami’o’i da sauran manyan makarantu a fadin ƙasar, domin faɗaɗa damar samun ilimi da kuma tabbatar da haɗin kai a fagen ilimi.

Wannan sanarwa ta fito ne a cikin wata takardar manema labarai da Boriowo Folasade, Daraktar Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, ta fitar a ranar Talata. Ta bayyana cewa wannan shiri yana ƙarƙashin jagorancin Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa.

A cewar sanarwar, wannan gyara yana cikin muhimman matakan aiwatar da manufar Renewed Hope Agenda ta gwamnati, wanda ke da nufin bai wa kowa damar samun ilimi mai zurfi tare da kiyaye ingancin karatu.

Ma’aikatar ta bayyana cewa an kawo wannan sabon tsari ne saboda tsofaffin dokoki masu tsauri da suka dade suna hana dimbin matasa samun gurbin karatu duk da cancantarsu.

Wannan sabon tsarin zai shafi jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha (polytechnics), kwalejojin ilimi, da makarantu masu kirkire-kirkire (Innovation Enterprise Academies – IEAs). Manufarsa ita ce warware matsalolin da suka jima suna haifar da rashin daidaito a tsarin ilimin gaba da sakandare a Najeriya.

A cikin sanarwar, Minista Dakta Alausa ya bayyana cewa an ga buƙatar wannan sauyi ne bayan shekaru da dama na takurawa ɗalibai, wanda ya sa masu cancanta da dama suka kasa samun gurbin karatu duk da nasarar da suka samu a jarrabawa.

Ya bayyana cewa fiye da dalibai miliyan biyu ke rubuta UTME a kowace shekara, amma kusan dalibai 700,000 kawai ake karɓa sakamakon matsin lambar dokokin shiga makarantu.

“Wannan rashin daidaito ba saboda rashin ƙwarewa ba ne, amma saboda tsohon tsarin da ya tsananta sharudda kuma ke toshe damar shiga makarantu,” in ji Ministan.

“Sabbin Ka’idojin Shigar Makarantu a Najeriya an tsara su ne domin kawar da shinge, tare da tabbatar da adalci da inganci.”

A ƙarƙashin sabon tsarin, za a buƙaci ɗalibai da ke neman shiga wasu shirye-shiryen karatu a jami’a, kwalejin fasaha, kwalejin ilimi da IEAs su samu kyakkyawan sakamako (credit pass) a ko dai Ingilishi ko Lissafi, bisa irin fannin da suke nema.

Haka kuma, dukkanin manyan makarantu za su daina ƙin sakamakon jarrabawar SSCE daga zama biyu (two sittings), domin duba daidaito da walwala ga masu neman gurbi.

Ministan ya ce tsohon tsarin da ke tilasta kowane ɗan takara ya samu credit a Ingilishi da Lissafi ya kasance babban cikas da ya hana dubban matasa samun damar shiga makarantu duk da cancantarsu.

Ya ƙara da cewa, wannan gyara yana da nufin tabbatar da cewa babu wani ɗalibi ɗan Najeriya mai ƙwazo ko sha’awar ilimi da zai rasa damar shiga makaranta saboda dokoki masu tsauri.