Tsohon Firayim Ministan Kenya, Raila Odinga, ya rasu yana da shekaru 80, kamar yadda iyalinsa suka shaida wa BBC.
Rahotanni sun nuna cewa Odinga ya rasu ne a ranar Laraba yayin da yake karɓar jinya a wani asibiti da ke ƙasar Indiya.
A ‘yan makonnin baya, an yi ta jita-jita kan lafiyarsa, duk da cewa iyalansa da abokan siyasa sun musanta labaran da ke cewa yana cikin matsanancin rashin lafiya. Bayan rasuwarsa, manyan shugabanni daga sassa daban-daban na duniya, ciki har da Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed, sun aika da sakonnin ta’aziyya.
Raila Odinga sananne ne a matsayin ɗan gwagwarmayar siyasa da jagora mai tasiri a harkokin siyasar Kenya. Ya tsaya takarar shugabancin ƙasa sau biyar, amma bai taɓa nasara ba. A duk lokacin da aka sanar da sakamakon zaɓe, Odinga kan yi zargin cewa an sace masa nasara.
A shekarar 2017, babbar kotun ƙasar Kenya ta tabbatar da korafinsa, inda ta soke nasarar Uhuru Kenyatta ta kuma umarci a sake gudanar da zaɓe. Duk da haka, Odinga ya ƙi shiga sabon zaɓen, yana neman a gudanar da sauye-sauyen tsarin zaɓe da farko.
Zaɓen da aka gudanar a 2007, wanda Odinga ya yi zargin an ci amanarsa ta hannun Mwai Kibaki, ya haddasa mafi munin rikici a tarihin Kenya. Rikicin ya haifar da tashin hankali a fadin ƙasar, inda mutane 1,200 suka mutu, kuma sama da mutane 600,000 suka rasa matsugunansu.
Don kawo ƙarshen rikicin, tsohon Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Kofi Annan, ya jagoranci yarjejeniyar raba mulki, wacce ta haifar da kafa gwamnatin haɗin kai, inda Raila Odinga ya zama Firayim Minista.
