Trends

Afuwar Maryam Sanda Ta Tunzura Zuciyoyin mu – Iyalin Bilyaminu Bello

Maryam Sanda tare da tsohon mijinta wanda ake zargin ta da kashewa

Iyalin marigayi Bilyaminu Ahmed Bello, wanda matarsa Maryam Sanda ta kashe a shekara ta 2017, sun bayyana babban bakin ciki da takaici kan afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Maryam Sanda ƙarƙashin ikon Prerogative of Mercy.

A wata sanarwa da Dr. Bello Haliru Mohammed, OFR (Dangaladiman Gwandu) ya sanya wa hannu a madadin iyalin, dangin Bilyaminu sun ce wannan mataki na afuwa ya buɗe tsofaffin raunuka kuma ya rushe adalcin da aka shafe shekaru ana nema ta hanyar kotuna.

Iyalin sun ce tun bayan wannan mummunan al’amari da ya faru a ranar Lahadi, 19 ga Nuwamba, 2017, sun zaɓi su zauna cikin shiru da mutunci, suna dogaro da tsarin shari’ar Najeriya domin neman adalci.

Sun ce dogaronsu ya sami sakamako ne a ranar 27 ga Janairu, 2020, lokacin da Babbar Kotun Abuja (FCT High Court) ta same ta da laifin kisa ta kuma yanke mata hukuncin kisa. Wannan hukunci, in ji su, ya samu sahalewa daga Kotun Daukaka Kara da kuma Kotun Koli a shekarun 2020 da 2023.

“Mun ji wani irin salama a zuciya lokacin da aka tabbatar da hukuncin, domin mun ɗauka cewa adalci ya samu, ko da kuwa ba zai cika ba,” in ji sanarwar.

Iyalin sun ce duk da cewa Maryam Sanda ba ta nuna nadama ba a duk tsawon shari’ar, sun rungumi hukuncin kotu da juriya, suna ƙoƙarin ci gaba da rayuwa bayan rasuwar ɗan’uwansu.

Sai dai sun nuna bakin ciki cewa wannan afuwa daga Shugaban Ƙasa, wanda ta haɗa da wasu mutane 175 ciki har da waɗanda ke kan layin hukuncin kisa, ta karya musu zuc