A cikin wani lamari da ya ba da mamaki, Alhaji Ahmed Bello Isa, mahaifin marigayi Bilyaminu Bello, wanda matarsa Maryam Sanda ta kashe shi a shekarar 2017, ya bayyana farin cikinsa bisa afuwar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Maryam.
Wannan mataki ya nuna irin haƙuri, tausayi da ƙarimci da Alhaji Isa ya nuna, wanda ya ce ya dade yana ƙoƙarin ganin an sake Maryam daga gidan yari.
Yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja tare da mahaifin Maryam, Alhaji Garba Sanda, Isa ya bayyana cewa tun bayan da kotu ta yanke wa Maryam hukuncin kisa, ya fara neman hanyoyin samar mata da ‘yanci cikin natsuwa da addu’a.
Ya ce dalilinsa na yafiya ya samo asali ne daga tausayin ɗan Adam, ba siyasa ba, yana mai cewa yana son a sake Maryam domin ta kula da ‘ya’yanta biyu ƙanana, domin kashe ta ba zai dawo da ɗansa ba.
“A matsayina na Musulmi mai cikakken imani, na karɓi abin da ya faru a matsayin ƙaddara, kuma na dade da yafe mata, na bar hukunci a hannun Allah,” in ji shi.
Rahotanni sun kuma nuna cewa Alhaji Isa tun a baya ya rubuta wasiƙu zuwa ga Ministan Shari’a na ƙasa a wancan lokaci, Abubakar Malami (SAN) da kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda na FCT a shekarar 2019, yana neman a yi wa Maryam Sanda afuwa, kamar yadda jaridar THISDAY ta tabbatar da hakan daga wasiƙun da aka gani.
Ko da yake ba a mayar masa da martani kan waɗannan buƙatun na farko ba, afuwar da Shugaba Tinubu ya bayar kwanan nan ta hanyar Presidential Prerogative of Mercy ta cika burinsa bayan shekaru da dama.
Alhaji Isa ya ce ya fara roƙon a sake Maryam tun kafin kotu ta tabbatar da hukuncin kisa a Janairu 2020.
Ya tuna yadda ya rubuta wa Kwamishinan ‘Yan Sanda wasiƙa a ranar 17 ga Janairu, 2019, inda ya bayyana cewa ya yafe wa duk wanda ke da hannu a mutuwar ɗansa, tare da roƙon a janye ƙarar, “domin ruhin ɗana ya huta cikin salama kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.”
Haka kuma, ya rantse da takardar rantsuwa (affidavit) a gaban Babbar Kotun FCT a ranar 21 ga Yuni, 2019, inda ya sake tabbatar da yafiyarsa da kuma roƙon a janye shari’ar gaba ɗaya.
