Wata mata mai shekara 25 daga Ho, Ghana, ta shiga hannun hukuma bayan da ake zarginta da ƙonawa ɗanta mai shekara 11 da wuta ta hanyar amfani da ƙarfen guga saboda biro da ya ɓace.
Wacce ake tuhuma, Jemima Kwaku, mai sana’ar girki ce, kuma an gurfanar da ita a gaban kotun majistire ta Ho bisa laifin jikkata mutum. Ta musanta laifin a kotu, amma aka umarci a ci gaba da tsareta har zuwa ranar 19 ga watan Agusta, 2025, lokacin da shari’ar za ta ci gaba yayin da bincike ke gudana.
A cewar masu gabatar da ƙara, lamarin ya faru ne a ranar 15 ga watan Yuli, 2025 a gidan iyalin. Yaron ya bayyana wa mahaifiyarsa cewa ɗan makaranta ya aro biro ɗin bai dawo da shi ba.
Amma mahaifiyar, wacce bata yarda da bayani ba, ta kulle shi a ɗaki sannan ta dumama ƙarfen guga ta danna masa a jiki. Wannan ya haifar masa da raunuka a ciki, ƙirji, leɓe, kafaɗu, baya da kuma bayansa. Daga bisani, ta umarce shi da kada ya sanar wa kowa.
Lamarin ya bayyana ne a ranar 18 ga watan Yuli lokacin da malamansa a makaranta suka lura da canjin halinsa, inda suka tambaye shi abin da ya faru. Sai ya bayyana musu gaskiya, kuma shugaban makarantar ya sanar da ’yan sanda.
An kai yaron asibiti an bashi kulawar lafiya, yanzu kuma yana ƙarƙashin hukumar jin daɗin al’umma (Social Welfare), inda yake murmurewa tare da samun tallafin jinya da na tunani.
Alkalin kotun, Mai shari’a Felix Datsomor, ne ya jagoranci zaman, yayin da ASP Noah Amuzu ya jagoranci masu gabatar da ƙara, inda ya roƙi kotu ta tsare wacce ake tuhuma har sai an kammala bincike. Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa 19 ga watan Agusta, 2025.
Wannan mummunan lamari ya tayar da ƙura a tsakanin masu kare haƙƙin yara da jama’a baki ɗaya, inda aka jaddada matsalar cin zarafin yara.
Ba wannan ne karon farko irin wannan ya faru a yankin ba. A watan Mayu 2024, wata mata mai shekara 62 ma an gurfanar da ita a kotu bayan da ta kona jikokin nata mai shekara 9 da ƙarfen guga saboda ta kasa sayar da naman tsire. Ita ma an mika ta ƙarƙashin hukumar jin daɗin al’umma.
Kungiyoyin kare haƙƙin yara sun yi amfani da wannan dama wajen jan hankali cewa hukunci da tashin hankali kan yara babbar barazana ce ga lafiyarsu, tare da jaddada cewa tarbiyya tana da muhimmanci, amma bai kamata ta zo da haɗarin lalata lafiyar yaro ba.







