Fitaccen tsohon ɗan wasan Chelsea kuma tauraron kwallon kafa na Afirka, Didier Drogba, ya kai wata takardar ƙorafi mai shafi fiye da shafuka 50 ga kungiyar Atalanta a Italiya, wacce Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta amince da ita, domin neman a gudanar da tsarin canjin Ademola Lookman cikin gaskiya da adalci.
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake samun rikici kan batun canjin Lookman, wanda ke neman barin Atalanta zuwa Inter Milan.
Drogba, wanda ya mika ƙorafin a Italiya, ya jaddada muhimmancin adalci da gaskiya a harkar cinikin ‘yan wasa, musamman idan ya shafi fitattun ‘yan wasan Afirka.
Lookman, wanda ya lashe lambar yabo ta gwarzon dan wasan Afirka na shekarar da ta gabata, ya nuna ƙudurin sa na komawa Inter Milan, inda rahotanni suka ce ya riga ya cimma matsaya da kulob ɗin tun makonni da suka gabata.
Inter Milan ta gabatar da tayin siyan sa har sau da dama, ciki har da na miliyan Yuro €45 tare da ƙarin kuɗaɗe, amma Atalanta ta ki amincewa.
A cewar Atalanta, an yi alkawari tun bara cewa idan za a sayar da Lookman to sai ga wani kulob daga wajen Italiya, domin guje wa ƙara ƙarfafa masu hamayya a gasar Serie A.
Lamarin ya tsananta, inda rahotanni suka bayyana cewa Lookman ya daina halartar atisaye na Atalanta fiye da mako guda kuma ya goge duk wata alaka da kulob ɗin daga shafukan sada zumunta.
Ƙungiyar kwallon kafa ta Najeriya ma ta fito fili tana goyon bayan Lookman wajen neman sauya sheka.
Sai dai duk da ƙin amincewar Atalanta, rahotanni na cewa Inter Milan na shirin gabatar da sabon tayin da zai kai kusa da bukatar Atalanta na miliyan Yuro €55, domin kammala cinikin kafin ƙarshen watan Agusta.
Lookman ya mika takardar neman canja sheka tare da yin jawabi a bainar jama’a yana mai cewa Atalanta ta yi masa alkawarin barinsa ya koma wani sabon kulob a wannan bazarar.







