Kuɗaɗen haraji da ake karɓa a Najeriya da aka danganta da kuɗin waje sun ƙaru sosai zuwa naira tiriliyan ₦6.33 a shekarar 2025, bisa bayanan da National Bureau of Statistics (NBS) ta fitar.
Adadin ya nuna ƙaruwa da kashi 27.3% idan aka kwatanta da naira tiriliyan ₦4.97 da aka samu a shekarar 2024, abin da ke nuna yadda gwamnati ke ƙara dogaro da kuɗaɗen da ke da alaƙa da kasuwannin waje a daidai lokacin da naira ke fuskantar sauye-sauye.
Binciken ya nuna cewa kuɗaɗen harajin da aka biya da kuɗin waje sun kai kashi 35.5% na jimillar harajin VAT da CIT, waɗanda suka kai naira tiriliyan ₦17.83 a shekarar 2025.
Harajin VAT ya ƙaru daga naira tiriliyan ₦6.72 a 2024 zuwa ₦8.61 a 2025, yayin da harajin kamfanoni (CIT) ya tashi daga ₦7.66 zuwa ₦9.22. Daga cikin wannan, VAT na kuɗin waje ya kai ₦2.10 tiriliyan, yayin da CIT na kuɗin waje ya kai ₦4.23 tiriliyan.
Bayanan rabin shekara na CIT sun nuna sauye-sauye: ₦1.34 tiriliyan a zangon farko (Q1), ya ragu zuwa ₦469 biliyan a Q2, ya sake tashi zuwa ₦1.75 tiriliyan a Q3, kafin ya daidaita zuwa ₦668 biliyan a Q4.
Masana sun ce ƙaruwa a ɓangaren kuɗaɗen waje na nuna yadda tattalin arzikin Najeriya ke karkata zuwa fannoni da ke samun kuɗaɗe a dala, kamar man fetur da iskar gas, sadarwa, harkokin kuɗi da kuma masu fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
Sabon tsarin canjin kuɗi na naira da ya dace da kasuwa ya ƙara darajar kuɗaɗen mu’amaloli na waje a cikin gida, wanda hakan ya taimaka wajen haɓaka kuɗaɗen haraji.
Haka kuma, VAT na shigo da kaya ya ƙaru daga ₦1.59 tiriliyan zuwa ₦2.03 tiriliyan, yayin da VAT na cikin gida (ban da shigo da kaya) ya kai ₦4.48 tiriliyan.
Biyan harajin kamfanoni na cikin gida ma ya tashi zuwa ₦4.99 tiriliyan, amma saurin ƙaruwa a ɓangaren kuɗaɗen waje na nuna wani sabon sauyi a tsarin harajin Najeriya, inda ake ƙara dogaro da fannoni da ke hulɗa da kasuwannin duniya.





