Hukumar kula da harkokin magunguna ta Najeriya, Pharmaceutical Council of Nigeria (PCN), ta rufe wuraren sayar da magunguna 131 a Jihar Nasarawa bisa laifin karya ƙa’idojin aiki.
Shugaban sashen sa ido da bin doka na hukumar, Dakta Suleiman Chiroma, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a ƙaramar hukumar Karu bayan kammala wani aikin sintiri na kwanaki uku.
Chiroma ya ce an gudanar da wannan aiki ne tsakanin 30 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu, 2026, bisa tsarin dokokin rarraba magunguna na ƙasa.
“Ta hanyar sintiri, bincike, sa ido da aiwatar da doka, PCN na samun gagarumar nasara wajen kawar da marasa ƙwarewa a harkar magunguna da kuma hana ajiya marar inganci,” in ji shi.
A cewarsa, an binciki wurare 272, ciki har da dillalan magunguna, kantunan magunguna na al’umma, shagunan sayar da ƙananan magunguna, da kuma wuraren da ba su da lasisi. Daga cikinsu, an rufe 131 — dillalai 16, kantunan magunguna 31, shagunan sayar da ƙananan magunguna 51, da kuma wurare 32 marasa lasisi.
Haka kuma, an bayar da umarnin gyara guda bakwai, yayin da aka kama wani likitan magunguna guda ɗaya bisa zargin hana jami’an bincike gudanar da aikinsu.
Laifukan da aka gano sun haɗa da rashin gabatar da lasisi, gudanar da aiki ba tare da izini ba, yin aikin likitanci ba bisa ka’ida ba, da kuma rashin tsaro wajen adana magungunan guba.
Chiroma ya bayyana cewa kashi 70 cikin 100 na wuraren da aka rufe suna cikin ƙaramar hukumar Karu, inda aka gano yawancin likitocin magunguna ba sa wurin aiki, suna barin masu taimako marasa ƙwarewa su riƙa gudanar da ayyuka.
“Mun lura da damuwa cewa kashi 70 cikin 100 na likitocin magunguna ba su halarta a wuraren aiki ba a cikin kantuna 86 da aka ziyarta, lamarin da ke rage ingancin kulawar lafiya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa kashi 61 cikin 100 ba su nuna lasisinsu kamar yadda doka ta tanada ba, yayin da yawancin masu sayar da ƙananan magunguna ke wuce iyakar abin da lasisinsu ya ba su dama.
Chiroma ya tabbatar da cewa PCN za ta ci gaba da tsaurara sa ido domin tabbatar da cewa ana sayar da magunguna cikin tsaro ta hannun ƙwararru.
“PCN na shawartar jama’a da su riƙa sayen magunguna kawai daga wuraren da aka bincika, aka amince da su, kuma aka yi musu rajista yadda ya kamata,” in ji shi.
Ya kuma jaddada kudurin hukumar ƙarƙashin jagorancin magatakarda, Pharm Ibrahim Ahmed, na bin manufofin Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da kuma shirin Shugaba Bola Tinubu na Renewed Hope Agenda, domin tabbatar da cikakken samun kulawar lafiya ga ‘yan Najeriya.

