Jarabawar Neco: Fursunoni 58 Suka Zana a Gidan yarin jihar Kano
Hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali a Najeriya NCoS reshen jihar Kano ta bayyana yadda fursunoni 58 suka zana jarabawar kammala Sakandire ta ƙasa NECO a shekarar nan. Kakakin gidan gyaran halin na jihar Kano Musbahu Kofar-Nasarawa ya shaidawa manema labarai a jiya Lahadi cewa yanzu haka fursunonin waɗanda ke tsaka da wa’adinsu…
