Najeriya ta fara taka muhimmiyar rawa a matsayin madadin mai samar da man jiragen sama ga Turai, yayin da rikicin Amurka da Iran ke kawo cikas ga hanyoyin samar da mai daga Gabas ta Tsakiya.
Wani jigilar mai na baya-bayan nan daga matatar Dangote Petroleum Refinery zuwa ƙasar United Kingdom ya nuna yadda Turai ke ƙara dogaro da matatun mai na Afirka ta Yamma.
Ana kiyasta cewa Turai na samun kusan kashi 40 cikin 100 na man jiragen sama ne ta mashigar Strait of Hormuz, amma tashin hankalin yankin ya sa farashin man a arewa maso yammacin Turai ya haura zuwa dala $1,744 kan kowace ton—kusan ninki biyu idan aka kwatanta da kafin yaƙin.
Wata majiya daga matatar Dangote ta shaida wa jaridar The Punch cewa, “Yawancin ƙasashen Turai su ne manyan masu sayenmu,” tana mai nuni da yadda farashi ya yi tashin gwauron zabi.
Bayanan masana’antu sun nuna cewa jigilar man daga Najeriya na nuna sauyin hanyoyin samar da mai, inda masu saye a Turai ke neman sabbin hanyoyi sakamakon fargabar ƙarancin mai.
Wani masani daga kamfanin Kpler, Matt Stanley, ya ce tsarin samar da mai ba ya tsayawa, sai dai yana sauya hanya ne kawai, yana mai cewa lamarin ya fi shafar yadda ake sauya hanyoyin jigilar kaya da kuma daidaita farashi, ba wai ƙarancin mai kai tsaye ba.
Sai dai masana sun yi gargaɗi cewa kamfanonin jiragen sama za su iya fara jin tasirin wannan yanayi nan ba da jimawa ba. Janiv Shah na kamfanin Rystad Energy ya ce ana ganin cewa ƙarancin mai na iya tasowa a wasu ƙasashe, tare da ƙarin farashi da zai shafi dukkan sarkar samar da kayayyaki.
Matatar Dangote, wadda ke aiki da cikakken ƙarfin tace ganga 650,000 a rana, ta fitar da kaya guda 12 da suka kai tan 456,000 na man da aka tace zuwa ƙasashen Afirka ta Yamma da kuma kwanan nan zuwa Birtaniya.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce masana’antar makamashi ta Afirka ba za ta ci gaba da fitar da albarkatun ƙasa kawai ba tare da shigo da kayayyakin da aka gama ba, yana mai jaddada muhimmancin dogaro da kai a fannin masana’antu.
Dogaro da Turai ga man Gabas ta Tsakiya, tare da raguwar shigo da mai daga Rasha da kuma durƙushewar matatun cikin gida, ya sa matatun Afirka ta Yamma suka zama masu matuƙar muhimmanci.
Wani masani daga Insights Global, Lars van Wageningen, ya ce masu saye a Turai za su ci gaba da komawa ga matatun Afirka ta Yamma, ciki har da Dangote, domin cike gibin da aka samu.
Masana sun ce wannan ci gaba na nuna yadda Afirka ta Yamma ke tasowa a matsayin muhimmiyar cibiyar samar da mai, wadda ke taimaka wa Turai rage dogaro da Gabas ta Tsakiya, tare da ƙarfafa rawar yankin a tsaron makamashi na duniya.
