Trends

Gwamnatin Neja Za Ta Fito da Sabbin Dokokin Wa’azin Addini

Gwamnan Niger, Umar Bago

Gwamnatin Jihar Neja ta fito da sabbin dokoki da ke tilasta malaman addini su gabatar da rubutattun hudubobinsu kafin su yi wa’azi a bainar jama’a, a matsayin mataki na dakile tayar da hankali da kuma inganta wa’azi mai tsafta.

Gwamna Umar Bago ne ya bayyana hakan a cikin shirin Politics on Sunday da aka watsa a tashar TVC. Ya bayyana cewa wannan ba haramta wa’azi ba ne, illa dai wani matakin kariya don tabbatar da cewa sakonnin da ake isarwa daga minbari ba su dauke da tunzura rikici, tsattsauran ra’ayi ko kuma adawa da gwamnati.

“Ban hana bishara ba,” in ji Bago. “Amma duk wanda yake son yin wa’azi—ko ranar Juma’a, Lahadi ko kowace rana—dole ya gabatar da rubutacciyar hudubarsa domin dubawa. Wannan dabi’a ce ma da ake amfani da ita a kasashe irin su Saudiyya.”

Ya jaddada cewa kasancewa malamin addini ba yana nufin a yi amfani da minbari wajen yada sakonnin da za su iya tayar da hankali ko kawo rabuwar kai ba. “Ba za ka iya amfani da minbari ka yi abin da ya saba wa al’umma ko gwamnati, sannan ka ce abu ne da ya dace ba,” in ji shi.

Don tabbatar da bin wannan doka, gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da hukumomin tsaro daban-daban ciki har da DSS, ‘yan sanda, NSCDC da kuma rundunar soji.

Baya ga duba huduba, gwamnati na kaddamar da tsarin lasisin wa’azi. Shugaban Hukumar Al’amuran Addini na jihar, Umar Farooq, ya tabbatar da cewa dukkan malamai dole ne su mallaki lasisin wa’azi cikin watanni biyu masu zuwa.

“Eh, jihar ta kafa doka kan wa’azi,” in ji Farooq. “Duk wanda yake son yin wa’azi dole ne ya nemi lasisi. Tsarin ya hada da karbo da cike fom a ofishinmu sannan a gurfana a gaban kwamitin tantancewa kafin a amince da shi.”

Gwamnatin ta ce wadannan matakan sun zama wajibi domin tabbatar da zaman lafiya, hana yaduwar tsattsauran ra’ayi da kuma tabbatar da cewa koyarwar addini na daidaita da manufar tsaro da daidaituwar zamantakewa a jihar.