Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin ta ki sauraron bukatar da jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya shigar, inda yake neman a kwashe shi daga tsarewar Hukumar Tsaro ta DSS zuwa Asibitin Kasa da ke Abuja domin samun kulawar gaggawa.
Mai shari’a Musa Liman, wanda yake alkalin hutu, ya bayyana cewa ikon da aka ba shi na sauraron shari’o’i a lokacin hutu ya kare a ranar Litinin, don haka ba shi da hurumin ci gaba da sauraron wannan sabuwar bukata. Ya umarci a mayar da takardun shari’ar zuwa ofishin babban alkalin kotun domin a sake bai wa wani alƙali.
A yayin zaman kotun, lauya mai kare Kanu, Uchenna Njoku (SAN), ya shaida cewa an shigar da bukatar a ranar 1 ga Satumba, amma gwamnatin tarayya wadda Asiwaju Adegboyega Awomolo (SAN) ya wakilta ta mika musu doguwar takarda mai shafi 37 a gaban kotu. Njoku ya nemi a dage zaman domin ya samu lokaci ya mayar da martani.
Awomolo bai yi adawa da bukatar dage zaman ba, inda ya bayyana cewa yana shirye ya bayyana a duk lokacin da aka sake tsara rana.
A cikin hukuncin gajere, Mai shari’a Liman ya nuna cewa lamarin yana da gaggawa ganin batun lafiya, inda ya ce zai shawarci babban alƙali ya hanzarta sake bai wa wani alƙali shari’ar.
Lauyan Kanu, Chief Kanu Agabi (SAN), ya shaida wa kotu cewa lafiyar wanda yake karewa ta tabarbare a hannun DSS, inda gwaje-gwajen likitoci suka gano matsala a hanta, pancreas, raguwar sinadarin potassium a jiki da kuma kumburi a ƙasan hannu.
Ya kara da cewa likitoci sun bada shawarar gaggauta tura shi Asibitin Kasa, amma wasikar da aka aika ga babban daraktan DSS kan wannan batu ba ta sami amsa ba. Ya ce amincewa da bukatar ba zai cutar da bangaren masu shigar da kara ba.
Emmanuel Kanu, kanin jagoran IPOB, ya rantsar da takarda a matsayin shaida, inda ya tabbatar da cewa likitocin da suka duba shi a watan Agusta sun gano matsalolin lafiya da ke bukatar kulawa ta gaggawa.
A halin yanzu, Kanu na fuskantar tuhumar ta’addanci a gaban Mai shari’a James Omotosho a shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CR/383/2015. Bukatar belin da aka shigar tun watan Mayu har yanzu ba a saurare ta ba saboda hutun shekara na kotu.
Bayan karewar ikon Mai shari’a Liman na shari’ar hutu, ana sa ran babban alƙalin kotun zai sake rarraba wannan bukata domin ci gaba da sauraro.
