NRS Ta Kaddamar da Tsarin Hadadden Lambar Haraji a Fadin Najeriya

Hukumar Tara Haraji ta Najeriya, Nigeria Revenue Service, tare da hadin gwiwar Joint Revenue Board, sun kaddamar da sabon tsarin hadadden lambar shaidar masu biyan haraji (Tax ID) ga dukkan masu biyan haraji a fadin kasar nan.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Litinin, ta bayyana cewa an kafa sabon tsarin ne bisa tanadin Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya ta shekarar 2025, wadda ta wajabta wa duk wani mai biyan haraji mallakar lambar Tax ID.

Hukumar ta ce sabon tsarin zai taimaka wajen karfafa gudanar da harkokin haraji, inganta gaskiya da kuma bunkasa ayyukan hidima ga masu biyan haraji.

“Sabuwar lambar Tax ID za ta zama hadaddiyar shaidar masu biyan haraji, wadda za ta saukaka mu’amala tsakanin masu biyan haraji da hukumomin haraji na tarayya da jihohi,” in ji sanarwar.

A cewar NRS, tsarin zai hada bayanan masu biyan haraji wuri guda, tare da kawar da maimaita bayanai da kuma saukaka hanyoyin rajista, cike takardu da biyan haraji. Haka kuma zai taimaka wajen gano bayanan masu biyan haraji cikin sauki domin rage asarar kudaden shiga da kuma kara tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Sabon tsarin zai maye gurbin tsohon tsarin tabbatar da lambar haraji na TIN Validation API da hukumomin gwamnati, bankuna da sauran cibiyoyi ke amfani da shi. Hukumomin da ke bukatar hadewa da sabon tsarin an umurce su da su tuntubi sashen Standardisation and Modernisation na JRB ko kuma sashen Tax Automation na NRS.

Hukumar ta kara da cewa mutane za su iya amfani da lambar shaidar zama dan kasa ta NIN a matsayin Tax ID, yayin da kamfanonin da ke rajista za su yi amfani da lambar rajistar Corporate Affairs Commission (RC Number).

Jami’an hukumar sun bayyana cewa wannan sauyi ya yi daidai da tanade-tanaden Dokar Kudi ta shekarar 2019, wanda yanzu aka kara karfafa shi a karkashin Dokar NTAA. Sun ce tsarin zai taimaka wajen hada bayanan masu biyan haraji a dukkan matakan gwamnati.

Hukumar ta jaddada cewa sabon tsarin hadadden Tax ID zai kara inganta gaskiya, saukaka bin dokokin haraji da kuma kyautata hadin kai tsakanin hukumomin haraji a Najeriya, lamarin da ake sa ran zai taimaka wajen kara kudaden shiga da kuma inganta ayyukan gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *