NCDC ta yi Gargadin Ƙara Yaɗuwar Cutar Sankarau a Arewacin Najeriya

Hukumar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Najeriya (NCDC) ta yi gargadi kan ƙara tsananta barkewar cutar sankarau a jihohin arewacin ƙasar, wanda ake dangantawa da kwayar cutar Neisseria meningitidis nau’in C, wadda alluran rigakafi na yanzu ba sa bayar da cikakkiyar kariya a kanta.

Babban Daraktan hukumar, Dakta Jide Idris, ya bayyana haka a Abuja yayin taron kwamitin kula da Asusun Samar da Kiwon Lafiya na Ƙasa karo na 14, inda ya ce yara masu shekaru tsakanin 1 zuwa 15 su ne suka fi kamuwa da cutar.

Ya bayyana cewa nau’in C ya maye gurbin nau’in A a matsayin wanda ya fi yaɗuwa, yayin da sauran nau’ikan kamar W, X da Y ke haifar da ƙananan lokuta. Ya ƙara da cewa cunkoso da kuma iska mai ɗauke da ƙura a lokacin rani na taimakawa wajen ƙara yaɗuwar cutar, musamman a yankin da ake kira “meningitis belt”.

Idris ya ce a halin yanzu Najeriya na cikin lokacin haɗari (daga Disamba zuwa Afrilu), inda yaɗuwar cutar ke ƙaruwa sakamakon rashin isasshen iska a wurare da kuma yanayi mai ƙura. Ya jaddada cewa duk da muhimmancin allurar rigakafi, akwai buƙatar ƙarin matakai domin shawo kan cutar.

Hukumar NCDC ta ƙara tsaurara sa ido da gwaje-gwaje a matakin jihohi, tare da ƙoƙarin ƙarfafa ƙarfin ƙasa wajen gano da tabbatar da kamuwa da cutar.

Ya yi gargaɗi cewa cutar sankarau na iya tsananta cikin sauri kuma ta yi sanadin mutuwa cikin ‘yan sa’o’i idan ba a yi magani da wuri ba. Gano cutar da wuri da kuma fara maganin ƙwayoyin cuta (antibiotics) na taimakawa wajen ceton rayuka.

Dakta Idris ya buƙaci ‘yan Najeriya da su garzaya asibiti nan take idan sun ga alamomi kamar zazzaɓi mai tsanani, ciwon kai mai ƙarfi, taurin wuya, amai, rikicewar hankali, farfadiya ko jin haske yana damun ido, yana mai gargaɗin kada a ɗauka cewa zazzaɓi da ciwon kai kullum cutar malaria ce.

Ya kuma ba da shawarar a guji cunkoso, a tabbatar da samun iska mai kyau a wurare, a rufe baki da hanci yayin tari ko atishawa, a kuma guji raba kayan abinci, tare da ƙarfafa jama’a su shiga shirye-shiryen allurar rigakafi domin rage yaɗuwar cutar.