Matatar man fetur ta Dangote Petroleum Refinery ta sanar da rage farashin man jiragen sama na Jet A1 daga Naira 1,750 zuwa Naira 1,650 kan kowace lita, matakin da ake ganin zai rage wa kamfanonin jiragen sama na Najeriya radadin tsadar aiki.
Kamfanonin jiragen sama sun yi gargadin yiwuwar dakatar da ayyukansu sakamakon tashin farashin man jirage, wanda ya tashi daga kusan Naira 900 kan kowace lita kafin rikicin Amurka da Iran zuwa tsakanin Naira 2,700 da Naira 2,900, yayin da wasu ‘yan kasuwa ke sayarwa har kan Naira 3,300.
A cikin sanarwar da matatar ta fitar, ta ce rage farashin ya zo ne tare da samar da damar bashi na kwanaki 30 ba tare da ruwa ba ga ‘yan kasuwa da kamfanonin jiragen sama, wanda bankuna za su tabbatar da shi.
Haka kuma, matatar ta bayyana cewa za a daina tsarin farashin da ake kayyade da dala, inda za a koma amfani da tsarin biyan kudin man da Naira.
“Dangote Petroleum Refinery ta rage farashin man jiragen sama na Jet A1 zuwa Naira 1,650 kan kowace lita domin rage matsin kudin aiki ga kamfanonin jiragen sama tare da tabbatar da wadataccen man fetur a fadin kasar nan,” in ji sanarwar kamfanin.
Masu ruwa da tsaki a bangaren sufurin jiragen sama sun dade suna gargadin cewa karin farashin Jet A1 na jefa kamfanonin jiragen sama cikin matsin tattalin arziki tare da barazana ga dorewar harkokin sufurin jirage a Najeriya.
Ana sa ran matakin da matatar Dangote ta dauka zai rage kudin sayen mai, ya daidaita ayyukan kamfanonin jiragen sama tare da taimakawa wajen rage tsadar kudin tikitin tafiya ga fasinjoji.
Masana harkokin sufurin jiragen sama sun bayyana cewa man jirage na daga cikin manyan abubuwan da ke cin kudaden kamfanonin jiragen sama, saboda haka wannan mataki zai taimaka wajen rage kalubalen gudanar da aiki a bangaren.
Masu sharhi kan tattalin arziki sun ce wannan mataki zai kara karfafa amincewa da karfin matatun mai na cikin gida tare da rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje, musamman a lokutan rikicin makamashi na duniya.

