Hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya ta haura kashi 20 cikin 100 a jihohi 11 a watan Afrilun 2026, lamarin da ke kara matsin tattalin arziki ga iyalai da rage karfin sayen jama’a.
Sabbin bayanan da National Bureau of Statistics (NBS) ta fitar kan ma’aunin farashin kayayyaki na CPI sun nuna cewa hauhawar farashin abinci ta kai kashi 16.06 cikin 100, wanda ya dan zarce yawan hauhawar farashin kayayyaki gaba daya da ya tsaya a kashi 15.69 cikin 100. Wannan ne karo na farko tun watan Agustan 2025 da farashin abinci ya zarce yawan hauhawar farashin kayayyaki gaba daya.
Jihohin da suka fi fama da tashin farashin abinci sun hada da Enugu mai kashi 32.7 cikin 100, Kwara mai kashi 30.8 cikin 100, da Adamawa mai kashi 30.1 cikin 100.
Sai dai jihohin Borno da Jigawa da Taraba sun samu mafi karancin tashin farashin, inda Borno ta samu kashi 1.7 cikin 100, Jigawa kashi 6.2 cikin 100, yayin da Taraba ta samu kashi 7.2 cikin 100.
Sauran jihohin da hauhawar farashin abinci ya haura kashi 20 cikin 100 sun hada da Rivers, Delta, Bauchi, Edo, Zamfara, Gombe, Anambra da Benue.
NBS ta bayyana cewa tashin farashin ya samo asali ne daga karin kudin kayan abinci na yau da kullum kamar gero, garin doya, citta, naman sa, garin rogo (garri), doya, barkono, busasshen kifi, rogo, wake, dankali, tumatir, alkama, waken soya, dawa, ayaba da karas.
A bangaren karin farashi daga wata zuwa wata, jihohin Niger, Bauchi da Kogi ne suka fi samun hauhawar, inda Niger ta samu kashi 8.5 cikin 100, Bauchi kashi 6.8 cikin 100, sannan Kogi ta samu kashi 6.7 cikin 100. Kebbi ce ta samu mafi karancin karin farashi da kashi 0.2 cikin 100.
Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashi a yankunan karkara ta kai kashi 16.36 cikin 100, wanda ya fi na birane da ya tsaya a kashi 15.40 cikin 100, alamar matsalolin samar da kayayyaki da sufuri sun fi tsanani a karkara.
Kungiyar Famine Early Warning Systems Network (FEWS NET) ta yi gargadin cewa tsakanin mutane miliyan 16 zuwa 17 a Najeriya na iya bukatar tallafin abinci cikin gaggawa kafin watan Nuwamban 2026, lamarin da zai sanya Najeriya cikin kasashen da ake hasashen za su fi bukatar agajin jin kai a duniya.
Masanin tattalin arziki, Muda Yusuf, ya ce hauhawar farashin abinci ya kai kashi 16.06 cikin 100 yayin da hauhawar farashin sauran kayayyaki ya ci gaba da kasancewa a mataki mai tsanani da kashi 15.86 cikin 100.
Ya bayyana cewa manyan abubuwan da ke haddasa hauhawar farashin sun hada da abinci, sufuri, makamashi, kiwon lafiya da kuma ayyukan gidajen abinci. Ya gargadi cewa matsalolin tsarin tattalin arziki ne ke haddasa hauhawar farashin, ba wai yawan bukata daga jama’a ba.
Ita ma Daraktar Lagos Chamber of Commerce and Industry, Dakta Chinyere Almona, ta ce hauhawar farashin na ci gaba da rage karfin sayen jama’a tare da rage ribar kasuwanci, musamman ga masana’antu, kananan sana’o’i, ‘yan kasuwa da kuma gidaje masu karamin karfi.
Ta bukaci gwamnati da masu tsara manufofi su kara hada kai wajen aiwatar da gyare-gyaren da za su magance matsalolin samar da kayayyaki domin rage matsin rayuwa a kasar.

