Masu Koyar da Jinyar Gyaran Jiki Sun Yi Watsi da Tsarin Shirin Samar da Diploma

Ƙwararrun masu koyar da jinyar gyaran jiki (Physiotherapists) a Najeriya sun yi watsi da shirin ƙirƙirar shirye-shiryen karatun diploma da kuma matsayin technician a fannin, suna mai gargadin cewa hakan na iya jefa lafiyar marasa lafiya cikin haɗari tare da rage ingancin ayyukan kiwon lafiya.

A wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da Nigeria Association of Physiotherapy (NSP) da Association of Clinical and Academic Physiotherapists of Nigeria (ACAPN) suka gudanar, masana sun bayyana cewa aikin jinyar gyaran jiki na buƙatar cikakken horo a matakin jami’a domin tantance marasa lafiya, gano matsalolinsu da kuma ba su kulawar da ta dace.

Shugaban ACAPN, Farfesa Udoka Okafor, ya ce ƙungiyar ta yi watsi da wannan shiri saboda damuwarta kan jin daɗi da tsaron lafiyar marasa lafiya.

Ya ce, “Mutanen da ba su da isasshen ilimi a fannonin ilimin tsarin jiki, yadda gabobin jiki ke aiki da kuma ilimin cututtuka, bai kamata a ba su damar kula da marasa lafiya ba.”

Okafor ya ƙara da cewa an daina shirye-shiryen diploma a fannin tun ƙarshen shekarun 1980, lokacin da aka mayar da karatun jinyar gyaran jiki zuwa matakin jami’a. Ya ce abin mamaki ne a shekarar 2026 ana neman komawa tsarin da aka yi amfani da shi tun shekarun 1950.

A nasa ɓangaren, Shugaban NSP, Dakta Felix Odusanya, ya yi gargadin cewa tura mutanen da ba ƙwararrun masu jinyar gyaran jiki ba zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHC) na iya ƙara yawan masu aikin bogi, musamman a lokacin da ƙwararrun masu wannan sana’a da dama ke zaman rashin aikin yi.

Ya bayyana cewa Najeriya na da isassun ƙwararrun masu jinyar gyaran jiki, inda jami’o’i sama da 80 ke koyar da wannan fanni, tare da fitar da kimanin ɗalibai 2,500 a kowace shekara. Ya ce ana sa ran adadin zai kai kusan 8,000 a shekara cikin shekaru uku masu zuwa.

Odusanya ya ba da shawarar a gaggauta ɗaukar ƙwararrun masu jinyar gyaran jiki aiki ta hanyar shirye-shiryen horaswa (internship), aikin yi na National Youth Service Corps, ɗaukar su aiki a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da kuma ba su aikin dindindin a ma’aikatun gwamnati, maimakon ƙirƙirar sabbin matakan aiki masu ƙarancin ƙwarewa.

Ya kammala da cewa, “Matsalar Najeriya ba rashin ƙwararrun masu jinyar gyaran jiki ba ce, illa rashin ingantaccen tsari na ƙasa da zai tabbatar da ɗaukarsu aiki, riƙe su da kuma tura su zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da al’ummomi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *