Gwamnatin Jihar Gombe ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kula da Mata Masu Cutar Fitsarin Gaba (Obstetric Fistula) da kuma Cibiyar Kula da Yaran da ke Bukatar Agajin Gaggawa a Babban Asibitin Deba, da ke karamar hukumar Yamaltu-Deba.
Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe, Dakta Manassah Jatau, wanda ya jagoranci bikin kaddamarwar, ya bayyana cewa samar da cibiyoyin na daga cikin kudurin gwamnatin jihar na bai wa harkar lafiya muhimmanci. Ya ce gwamnatin ta riga ta aiwatar da shirye-shirye kamar bude cibiyoyin lafiya masu aiki na sa’o’i 24 a dukkan gundumomi 114 na jihar tare da fadada kayayyakin more rayuwa a bangaren lafiya.
Ya ce an gina Cibiyar Kula da Mata Masu Cutar Fitsarin Gaba ne da tallafin Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya, United Nations Population Fund (UNFPA), domin ba mata masu fama da wannan matsala cikakkiyar kulawa da magani, tare da dawo musu da mutunci da damar sake shiga cikin al’umma.
Haka kuma, ya ce Cibiyar Kula da Yaran da ke Bukatar Agajin Gaggawa an kafa ta ne domin rage mace-macen yara ta hanyar ba yara masu fama da tamowa kulawa ta musamman.
A cewarsa, “An samar da wannan cibiya ne domin dawo da mutunci, sake gina rayuwar mata masu fama da cutar fitsarin gaba, da kuma ba su damar dawo da kwarin gwiwa.”
Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Alhaji Ibrahim Jalo, ya bayyana cibiyoyin a matsayin wani babban ci gaba wajen tabbatar da kowa ya samu ingantaccen kiwon lafiya, yana mai cewa za su taimaka wajen inganta lafiyar mata masu juna biyu da kuma kare rayukan yara.
Wakilan UNFPA sun sake jaddada kudurinsu na ci gaba da tallafa wa Jihar Gombe, inda suka bayyana cewa karamar hukumar Yamaltu-Deba ce ke da mafi yawan masu fama da cutar fitsarin gaba a jihar. Sun ce hadin gwiwar da aka yi ya taimaka wajen yi wa mata sama da 151 magani a shekarar 2025.
Shi ma, Dakta Abubakar Umar, wanda ya kafa kungiyar Taimaka tare da wasu abokan aiki, ya ce cibiyar kula da yara tana da gadaje 203, likitoci bakwai da kuma sama da ma’aikatan jinya 50. Ya kara da cewa akwai shirin fadada ta zuwa gadaje 250, kuma za a ci gaba da ba dukkan yaran da ke bukatar kulawa magani kyauta.
Shugabannin al’umma ciki har da Sarkin Deba, sun yi kira ga iyaye da su guji auren yara kanana, wanda suka bayyana a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa cutar fitsarin gaba. Sun kuma yi alkawarin tabbatar da kula da cibiyoyin yadda ya kamata domin su ci gaba da amfani ga al’umma na dogon lokaci.



