Likitoci Sun Bukaci Ƙarin Matakai Don Yaƙi da Cututtukan da Ba Su Yaduwa

Ƙungiyar West African College of Physicians (WACP) reshen Najeriya ta yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma saka hannun jari a fannin kiwon lafiya domin tunkarar cututtukan da ba sa yaɗuwa (NCDs), ƙauracewar ƙwararrun likitoci zuwa ƙasashen waje da kuma yiwuwar bullar sabbin annoba a nan gaba.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Benjamin Uzochukwu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai gabanin babban taron shekara-shekara na 50 da kuma taron kimiyya na ƙungiyar da za a gudanar a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan.

Ya bayyana cewa cikin shekaru 50 da suka gabata, ƙungiyar ta horar da ƙwararrun likitoci 4,654 a fannoni shida da suka haɗa da Lafiyar Al’umma, Magungunan Iyali, Magungunan Cikin Gida, Kimiyyar Gwaje-gwajen Asibiti, Kula da Lafiyar Yara da kuma Ilimin Lafiyar Ƙwaƙwalwa. Ya ce hakan ya ba da gagarumar gudummawa wajen inganta harkokin kiwon lafiya a Najeriya da ma ƙasashen Yammacin Afirka.

A cewarsa, “Shekaru hamsin da suka gabata a Ibadan, wasu kaɗan daga cikin likitoci ne suka kunna fitila. Yanzu wannan fitilar ta zama haske mai ƙarfi da ke jagorantar horas da ƙwararrun likitoci a Najeriya da Yammacin Afirka. Hakkinmu shi ne mu tabbatar da wannan haske ya ci gaba da haskakawa tare da miƙa shi cikin ƙarfi ga tsara mai zuwa.”

Taron na bana mai taken “Gina Gada, Ƙarfafa Juriya da Haɗin Gwiwa a Fannin Lafiya” ya haɗa ƙwararru da masu tsara manufofi sama da 400 domin tattauna hanyoyin inganta ayyukan kiwon lafiya da horas da ƙwararrun likitoci.

Farfesa Uzochukwu ya kuma bayyana cewa ƙungiyar ta rungumi amfani da fasahohin zamani da suka haɗa da kiwon lafiya ta hanyar sadarwa (telemedicine), tsarin bayanan kiwon lafiya da kuma basirar wucin gadi (AI), yana mai jaddada muhimmancin sabunta tsarin horaswa tare da tabbatar da amfani da waɗannan fasahohi cikin aminci da ɗa’a.

Haka kuma, ya sanar da shirin gudanar da aikin ba da kulawar lafiya kyauta ga mazauna yankin Kasumu Ajia kimanin mutum 500, inda za a duba tare da yi musu maganin zazzabin cizon sauro, hawan jini, ciwon sukari, gyambon ciki, matsalolin haƙora da kuma ƙananan tiyata.

Ƙungiyar WACP ta yi gargadin cewa ci gaba da ficewar ƙwararrun ma’aikatan lafiya zuwa ƙasashen waje, matsin tattalin arziki da kuma bullar sabbin cututtuka na ci gaba da zama manyan ƙalubale ga fannin kiwon lafiya. Saboda haka ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin gina tsarin kiwon lafiya mai ƙarfi da ɗorewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *