Majalisar Wakilai ta amince da kasafin kuɗi na naira biliyan 479.5 ga Nigerian Communications Commission (NCC) domin shekarar kuɗi ta 2026.
Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin Sadarwa, wanda ya bayyana yadda za a rarraba kuɗaɗen hukumar daga Asusun Shigar Kuɗaɗen Doka, wanda ya haɗa da kuɗaɗen lasisi, kuɗin amfani da bakan mitoci (spectrum), harajin aiki na shekara-shekara, da sauran hanyoyin samun kuɗi na doka.
Daga cikin jimillar kuɗin, an ware naira biliyan 124.44 domin kashe kuɗaɗen yau da kullum (recurrent expenditure), inda naira biliyan 38.53 za su tafi albashi, naira biliyan 29.97 don kuɗaɗen ma’aikata, naira biliyan 28.45 don ayyukan gudanarwa, yayin da naira biliyan 11.53 za su tafi harkokin ofis.
Kuɗaɗen tafiye-tafiye sun kai naira biliyan 7.23, yayin da kuɗaɗen da suka shafi bakan mitoci suka kai naira biliyan 6.93.
An ware naira biliyan 26.78 domin ayyukan gina jari (capital expenditure), wanda ya haɗa da ayyukan cikin gida da kuma ayyukan tuntuba (consultancy). Haka kuma, an ware naira biliyan 32.01 domin ayyuka na musamman, ciki har da cibiyoyin sadarwar gaggawa (₦6.92bn), sa ido kan ingancin sadarwa (₦2.31bn), da shirye-shiryen tallafawa makarantu (₦10.79bn).
Sauran tanade-tanade sun haɗa da naira biliyan 2.02 don koyon ƙwarewar dijital, naira biliyan 2.23 don kula da bayanan masu amfani da layin waya, da naira biliyan 7.74 don ci gaba da wasu ayyukan tallafi.
Har ila yau, NCC za ta tura naira biliyan 20 zuwa Universal Service Provision Fund (USPF), sannan ta mayar da naira biliyan 276.28 a matsayin rarar kuɗi ga gwamnatin tarayya.
Ana sa ran manyan hanyoyin samun kuɗin za su haɗa da naira biliyan 250 daga harajin aiki na shekara-shekara, naira biliyan 192.89 daga kuɗin bakan mitoci, tare da ƙananan kuɗaɗe daga rajistar kayan sadarwa, lambobin waya, kuɗaɗen gudanarwa, da lasisi.
Shugaban Kwamitin, Peter Akpatason, ya ce kasafin ya nuna muhimmiyar rawar da NCC ke takawa wajen faɗaɗa ababen more rayuwa na dijital, tallafawa makarantu, da tabbatar da dorewar dokokin kula da harkar sadarwa a Najeriya.







