Maganin Nukiliya: Najeriya ta ƙaddamar da Sabon Shirin Yaƙi da Cutar Daji

Kiwon lafiya Kiwon lafiya

Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da muhimman takardu biyu na manufofi—Manufar Ƙasa kan Maganin Nukiliya da Tsarin Aiwatarwa, da kuma Shirin Ƙasa na Kula da Cutar Daji 2026–2030—da nufin ƙarfafa rigakafi, gano cutar da wuri, magani da kuma bincike kan cutar daji.

An bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na ministoci da aka gudanar a Abuja domin bikin Ranar Yaƙi da Cutar Daji ta Duniya 2026, inda Ƙaramin Ministan Lafiya da Jinƙai, Daktta Iziaq Adekunle Salako, ya yi gargaɗin cewa ƙaruwa mai yawa a yawan masu kamuwa da cutar daji a duniya na zama babbar barazana ga ƙasashe masu ƙaramin da matsakaicin tattalin arziƙi.

“A shekarar 2025 kaɗai, an gano kusan sabbin mutane miliyan 20 da ke dauke da cutar daji a faɗin duniya, inda sama da mutane miliyan 10 suka rasu,” in ji shi.

Salako ya jaddada cewa rigakafi shi ne mabuɗin yaƙi da cutar, yana mai cewa “fiye da kashi 40 cikin 100 na mutuwar masu cutar daji a duniya na da alaƙa da abubuwan haɗari da za a iya kauce musu, kamar shan taba, shan barasa, cin abinci da aka sarrafa fiye da kima, kiba, da gurɓatar iska.” Ya ƙara da cewa, “kusan rabin cututtukan daji za a iya hana su ta hanyar tsare-tsaren kiwon lafiyar jama’a.”

Ministan ya bayyana ci gaban da Najeriya ta samu ƙarƙashin Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda), ciki har da faɗaɗa ayyukan bincike da gwaje-gwajen gano cutar da wuri, da kuma zuba jari a kayan aiki da gine-ginen kula da cutar daji.

“An samar da na’urorin mammogram ga asibitoci a Abuja, Lagos, Benin, Enugu, Sokoto, Gombe, Kano da Ile-Ife. Yanzu ’yan Najeriya na iya yin gwajin gano cutar sankarar nono a kai a kai,” in ji shi.

Salako ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da haɗin gwiwa a matakin yanki, inda ya ce, “Najeriya na aiki tare da Masar da Kenya wajen kafa Cibiyar Haɗin Gwiwar Onkoloji ta Afirka,” yana mai cewa dandalin zai ƙarfafa tsarin kula da cutar daji a nahiyar Afirka ta hanyar musayar ilimi da ƙirƙira.

Haka kuma, ya ƙaddamar da shirye-shiryen gwajin cutar daji kyauta a duk faɗin ƙasar nan tsawon watan Fabrairu, da nufin duba akalla mutane 1,000 a kowanne yanki. “Rigakafi ba wai kawai ya fi magani ba ne, har ila yau ya fi araha; shi ne komai,” in ji Salako.

Shugaban Ƙungiyar Cutar Daji ta Najeriya, Farfesa Abidemi Omonisi, ya yi maraba da sabbin manufofin, amma ya yi gargaɗi cewa har yanzu akwai gibin adalci a fannin kula da cutar.

“Har yanzu da yawa daga cikin marasa lafiya na zuwa asibiti ne a makare, suna fuskantar tsadar kuɗin magani daga aljihunsu, tare da ƙarancin samun damar gwaje-gwaje da ayyukan kula da cutar daji,” in ji shi, yana mai jaddada buƙatar sanya rayuwar mutane—ba ƙididdiga kaɗai ba—a tsakiyar kulawar lafiya.

Omonisi ya buƙaci ƙarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, ƙungiyoyin farar hula da masu zaman kansu.

“Zuba jari a yaƙi da cutar daji ya kamata a gan shi ba a matsayin kashe kuɗi ba, sai dai a matsayin jajircewa wajen kare rayuwa, haɓaka aiki da bunƙasa ƙasa,” in ji shi, yana mai bayyana fatan ganin makoma inda cutar daji ba za ta ƙara zama hukuncin kisa ba.