Trends

Harin ’Yan Bindiga: Kebbi Ta Buɗe Makarantar GGCSS Maga Bayan Watanni Biyu

Makarantar Maga inda yan bindiga suka yi awun gaba da Dalibai mata 25

Gwamnatin Jihar Kebbi ta sake buɗe Makarantar Gwamnati ta ’Yan Mata ta Sakandare (Government Girls’ Comprehensive Secondary School – GGCSS), Maga, bayan shafe watanni biyu da ’yan bindiga suka kai hari makarantar.

Matakin ya biyo bayan harin da ’yan bindiga suka kai makarantar inda suka sace ɗalibai mata 24 tare da kashe Mataimakin Shugabar Makarantar. Bayan wannan lamari, gwamnati ta bayar da umarnin rufe makarantar nan take tare da wasu makarantu a yankin.

Da take ganawa da manema labarai bayan taron tsaro da shugabannin makarantu da daraktocin makarantu a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, a ranar Talata, Kwamishiniyar Ilimin Firamare da Sakandare, Dakta Halima Bande, ta ce makarantar ta shirya tsaf domin ci gaba da harkokin karatu.

Ta bayyana cewa an dawo da kwarin gwiwar iyaye da ɗalibai ta hanyar shawarwari (counseling) da kuma cikakken tura jami’an tsaro makarantar.
“Gwamnati ta tanadi dukkan matakan tsaro da suka dace domin tabbatar da lafiyar ɗalibai da ma’aikata,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa Gwamna Nasir Idris ya bayar da umarnin gudanar da shirye-shiryen wayar da kai kan tsaro ga shugabannin makarantu da ma’aikatan makarantu domin hana sake faruwar irin wannan lamari. Ta ce an riga an gudanar da irin waɗannan taruka a Zuru, Yauri, Jega, Bunza da Argungu, yayin da aka kammala na ƙarshe a Birnin Kebbi.

Dakta Bande ta jaddada cewa shugabannin makarantu, mataimakansu, ma’aikata da ɗalibai na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron makarantu.

“Ba za mu yarda ’yan bindiga su kwace mana tunanin zaman lafiya ba,” in ji ta. Ta kuma shawarci makarantu da su kula da kyakkyawar alaƙa da al’ummomin da ke kewaye da su, tana mai bayyana su a matsayin muhimman masu ruwa da tsaki a tsarin tsaro na yankunansu.

Ta kuma ba shugabannin makarantu shawarar su rika tuntuɓar hukumomin tsaro akai-akai domin samun shawarwari na ƙwararru kan harkokin tsaro, tare da jaddada muhimmancin ɗaukar matakan kariya tun da wuri.

Ta yabawa Gwamna Idris bisa amincewa da tura jami’an tsaro zuwa makarantu, tana mai cewa hakan ya ƙarfafa gwiwar malamai da ɗalibai wajen gudanar da harkokin karatu cikin kwanciyar hankali. Haka kuma ta yaba wa ’yan sanda, Hukumar Tsaron Farar Hula (NSCDC), da Hukumar Tsaron Ƙasa (DSS) bisa wayar da kan shugabannin makarantu kan tsaro da matakan kariya.

A nasa jawabin, Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da Ayyuka, ACP Yakubu Lawal Gumi, ya gargaɗi shugabannin makarantu da su guji sakaci da zai bai wa masu laifi damar shiga makarantu.

“Dole ne ku tafiyar da makarantu cikin tunanin tsaro. Ku tabbatar da wadataccen haske, domin masu laifi ba sa son bayyana, sannan ku kasance masu lura da duk wani mutum mai kawo shakku,” in ji shi.