Trends

NAFDAC Ta Janye Alluran Mivacron da Nimbex Saboda Yiyuwar Barazana ga Lafia

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC)

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta yi gargaɗi ga al’umma kan janye wasu rukunin allurar Mivacron Injection 0.2% da Nimbex Injection 2mg/mL sakamakon yiwuwar barazanar tsaro.

Ma’aikatar Lafiya ta Hong Kong ce ta amince da janye rukuni ɗaya na Mivacron (lambar rukuni: XPC19) da kuma rukunai biyar na Nimbex (lambobin rukuni: XP1SQ, XPC1G, XPC6W, XP1V5, XP1VF), waɗanda kamfanin Aspen Pharmacare Asia Limited ya ƙera.

Kamfanin GlaxoSmithKline ya gano matsalolin inganci a yayin duba magungunan da ido (manual visual inspection), inda ake zargin cewa ƙwayoyin gilashi a cikin ampuloli sun iya tsallake bincike ba tare da an gano su ba.

A sakamakon haka, kamfanin Aspen ya fara janye magungunan da kansa a matsayin matakin kariya domin kare lafiyar marasa lafiya. Duk alluran biyu — Mivacron (mivacurium) da Nimbex (cisatracurium) — ana amfani da su ne a matsayin kari ga maganin sa barci gaba ɗaya (general anaesthesia) a lokacin tiyata.

Ko da yake har yanzu ba a tabbatar da samun wata illa ga marasa lafiya ba, NAFDAC ta shawarci ma’aikatan lafiya da masu amfani da magungunan da su killace rukunin da abin ya shafa nan take.

Hukumar ta kuma buƙaci jama’a su rika kai rahoton duk wani magani da bai kai ƙa’ida ba ko na bogi zuwa ofisoshinta, ta hanyar lambar waya kyauta 0800-162-3322, ko ta imel tosf.alert@nafdac.gov.ng.