Wani mummunan gobara ya lakume wani ɗakin kwanan mata (Female Hostel Annex) a Jami’ar Jihar Gombe da yammacin Alhamis.
Shaidu sun ce gobarar, wacce ta tashi da misalin ƙarfe 9:30 na dare, ta tilasta wa daliban su tsere domin kare rayukansu, suna barin kayayyakinsu a ciki.
Rahotanni ya nuna cewa daliban maza da mata sun yi iya ƙoƙarinsu wajen kashe wutar kafin isowar jami’an kwana-kwana.
Ko da yake babu rahoton asarar rai ko raunuka masu tsanani, gobarar ta lalata wani sashi mai yawa na masaukin, inda dalibai da dama suka yi asarar kayayyaki.
Hukumomin jami’ar sun tabbatar da cewa an fara bincike domin gano musabbabin gobarar da kuma irin asarar da aka yi.
A cikin wata sanarwa, Jami’in Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Mista Hadu Ligari, ya ce an shawo kan lamarin.
“Wannan sanarwa ce ga al’ummar jami’a, iyaye, masu kula da ɗalibai da kuma jama’a gaba ɗaya cewa an samu gobara a ɗakin kwanan mata na jami’ar ranar Alhamis, 2 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 9:00 na dare.
“Mun yi godiya da cewa babu asarar rai, kuma an shawo kan lamarin. Hukumomin jami’ar suna ci gaba da tantance dalilan aukuwar lamarin da irin asarar da aka yi. Za a fitar da cikakken bayani a gaba,” in ji shi.
Wakilinmu ya tattaro cewa majiyoyi daga jami’ar sun bayyana yiwuwar gobarar ta samo asali ne daga iskar gas da ɗaliban ke amfani da shi wajen dafa abinci a cikin ɗakunan kwana.
Majiyoyin sun kuma ce kwanan nan ne hukumomin jami’ar suka janye takunkumin amfani da kwalayen gas a cikin ɗakunan kwana.
