Daga Idris Umar Feta
Abin da ya kamata ya kasance hanya mai sauƙi, ya koma tamkar mafarki mai ban tsoro a tsakiyar dare. Ga ma’aikatan da suka yi ritaya a Najeriya, samun hakkinsu na fansho ya zama cike da wahalhalu, cikas marasa ma’ana, da tsarin da yake kamar an tsara shi ne don takura musu ba taimakonsu ba.
A wannan zamani na fasaha, mutum zai yi tsammanin cewa mai ritaya zai iya samun fanshonsa cikin sauƙi, har ma daga nesa, ba tare da wahalar zuwa ofishi kullum ba. A karshe dai, duk tsawon aikin da suka yi, ma’aikata suna cike bayanai marasa iyaka, suna shiga tantancewa lokaci zuwa lokaci, suna kuma rubuta jarrabawar karin matsayi kafin su samu ci gaba.
Me ya sa duk wannan ba zai isa ba wajen sauƙaƙa musu a lokacin ritaya? Me ya sa shekarun ƙarshen aikin mutum za su zama cike da wahala? Gaskiyar magana ita ce: samun fansho a Najeriya sau da yawa yana buƙatar tafiya ofishin fansho kullum, sannan a dawo gida ba a samu wani sakamako ba. Na tuna ganin wani dattijo mai gashi fari, mai rauni, yana zaune a ofishin fansho bayan ƙarfe 5 na yamma, amma har yanzu ba a kula da shi ba.
Da murmushi mai rauni a fuskarsa, ya ce min: “Na san akwai yiwuwar ba za a kula da ni ba duk da cewa na jira wannan lokaci. Babu matsala, sai na dawo gobe.” Maganarsa da yadda ya nuna rashin ƙwarin gwiwa sun taɓa zuciyata ƙwarai. A gefe ɗaya kuma, wani tsoho ya daga murya cikin takaici.
Ya riƙe wayoyi biyu da suka karye yana cewa: “Ga wayoyi biyu nan sun lalace a lokacin da nake ta kai komo a banki don samun bayanan asusun da aka ce in kawo. Kuma don me? Fanshona fa ba wani abu ba ne da zai sa in wahala haka har in lalata wayoyi biyu.”
Bayan haka kuma, wata mata ta fito daga ofishin tana ta guntun magana da kanta: “Idan ba za ku bani kuɗina ba, ku riƙe shi kawai. Me ya sa kullum sai in dawo, in kashe kuɗin mota, sannan har yanzu ba na iya cika waɗannan buƙatu marasa iyaka?” Wannan maganar ta tuna min wani bidiyo daga Dubai, inda mace ta sabunta lasisin tuƙinta daga wata na’ura irin ATM cikin ƙasa da mintuna biyar.
Na tambayi kaina: me ya sa batun fansho, wanda yake da matuƙar muhimmanci ga rayuwar tsofaffin mu, ba zai kasance cikin sauƙi haka ba? Me ya sa za a ci gaba da takura musu da wahalar da ba dole ba?
Mun taba ganin rahotannin da suka nuna yadda tsoffin sojoji suka rika faduwa suna mutuwa a layi yayin da suke jiran fanshonsu. A da, idan ka wuce Zone 4 a Abuja, za ka ga tsofaffi da dama suna bara, wasu ma na kwana a waje, saboda fanshonsu ya makale watanni ko shekaru.
Waɗannan mutane ne da suka sadaukar da shekarun ƙuruciyarsu wajen bautar ƙasa, amma yanzu an bar su cikin rauni da yunwa. Ni ma na sha wahala irin wannan. Bayan na kai shekarar ritaya, na je babban ofishin Premium Pension Limited a Area 3 domin samun hakkina.
A rana ta farko, an bani jerin takardun da ake buƙata, na tafi cikin kwarin gwiwa cewa za a gama da ni cikin lokaci. Amma daga baya, kwarin gwiwa ya rikide ya koma takaici. Mako-mako suna wucewa, ina cikin wannan takardar ba ta ƙare ba, ina ta dawowa babu mafita.
Sau biyu na kasa ma mika takarduna saboda cunkoson mutane a ofishin. Yanayin wurin ya yi kama da kasuwa — tsofaffi na zaune a rana, wasu a cikin layi mai cunkoso a ciki, duk suna jiran a duba su.
A wani rana mai wahala, sai na samu damar zama da jami’in. Ya duba takarduna, sannan ya ce: “Alhaji, an ce a kawo bayanin asusu na kwanaki 90. Naka bai cika wannan sharadin ba.” Lokaci ya kusa 5 na yamma, kuma babu ƙarfi a jikina. Na tambaye shi: “Me ya sa ba za ku yi amfani da wanda na kawo ba?” Amma babu amsa. Na fahimci sai na sake komawa banki.
Wannan ya bani takaici ƙwarai. Na bar sauran harkokina gaba ɗaya don wannan fansho, amma har yanzu ana jefa ni daga gefe zuwa gefe tamkar ni ba ɗan ƙasa ba ne da ya cancanci mutunci.
Sannan tambaya ta sake dawowa: me ya sa ake buƙatar bayanin asusun kwanaki 90 da kuma pay slip na watanni uku daga tsohon wurin aiki, alhali dukkan bayanan aikin mutum da tarihin aikinsa suna cikin kundin gwamnati? Me ya sa ake tilasta wa tsofaffi irin wannan wahala?
Duniya na tafiya cikin saurin zamani. Kananan na’urori da manhajojin wayar hannu a wasu ƙasashe suna magance matsaloli cikin mintuna, alhali a nan tamu sai ya ɗauki makonni ko watanni. Ma’aikatan fansho ya kamata su kasance na farko wajen rungumar irin wannan sauƙi, saboda aikinsu ba wai kara wa masu ritaya wahala ba ne, sai dai sauƙaƙa musu.
Amma abin da muke gani akasin haka ne. Tsofaffi masu rauni suna shiga wahala don samun hakkinsu. Suna kashe kuɗin da ba su da shi a mota, suna tsayawa awoyi a layi, sannan su koma gida da ƙarin takardun da ake buƙata.
Haka bai kamata ya kasance ba. Fansho ba kyauta ba ce daga gwamnati ko masu gudanar da shi; hakkine da aka nema bayan shekaru na aiki. Tilasta wa tsofaffi wahala wajen samun shi tamkar ƙwace musu mutunci ne a lokacin da ya kamata a girmama su.
A karshe na fahimta: Premium Pension Limited, da dukkan tsarin fansho a Najeriya, dole su yi gyara. Ya kamata a samar da tsari da ya dace da mutuncin waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen bautar ƙasa.
Masu ritaya sun cancanci fiye da wannan wahala mara iyaka. Ina ganin Premium Pension na iya, kuma dole ya fi wannan.
Idris Umar Feta: findarumar@gmail.com
