Umarnin da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayar na rufe gidan rediyo na Badeggi FM da ke Minna, babban birnin jihar, ya haddasa tirjiya da fushin jama’a da kungiyoyi masu kare hakkin dan Adam.
Gwamna Bago ya umurci Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Neja da Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed (mai ritaya), da su rufe gidan rediyon tare da kwace lasisin aikinsa da kuma bincikar mai gidan rediyon.
A cewar Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Bologi Ibrahim, wanda ya fitar da sanarwa, gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a yayin taron fadada jam’iyyar APC na jihar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Minna.
Ibrahim ya bayyana cewa, gwamnan ya zargi gidan rediyon da yada shirye-shiryen da ke tayar da hankalin jama’a tare da zuga su kan gwamnati, sannan ya umurci jami’an tsaro da su rufe gidan da kuma gurfanar da mai gidan gaban hukuma.
“Gwamna Bago ya bayyana cewa, gidan rediyon na amfani da shirye-shiryensa wajen zuga jama’a da tayar da tarzoma. Ya kuma bukaci a kwace lasisin gidan rediyon gaba daya,” inji Ibrahim.
Martanin Gidan Rediyon Badeggi FM
Daraktan Ayyuka na Badeggi FM, Abubakar Shuaib, ya mayar da martani ga umarnin gwamnan, inda ya ce kamata ya yi gwamnati ta bi hanyar doka ta hannun Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin (NBC), maimakon amfani da jami’an tsaro wajen razana ma’aikata da mai gidan rediyon.
“Ya kamata gwamna ya rubuta korafi ga NBC domin gudanar da bincike. NBC na da jadawalin shirye-shiryenmu kuma ana sa ido a kansu kullum. Bai kamata a zargi mu da tayar da hankali ba domin muna kokarin bin ka’ida da rikon gaskiya,” inji Shuaib.
Tarihin Take Hakkin ’Yan Jarida a Jihar Neja
Rahotanni sun nuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da aka ci zarafin ’yan jarida a karkashin gwamnatin Bago ba.
A watan Nuwamba 2023, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Mohammed (mai ritaya), ya yi yunkurin karbe midget na wakilin Voice of America, Mustapha Nasiru Batsari, lokacin da ya je neman bayani dangane da rikicin da ke tsakanin Fulani da manoma Gbagyi a Beji, karamar hukumar Bosso.
Haka zalika, a watan Janairu 2025, an tsare wakilin jaridar People’s Daily da kuma shugaban kungiyar NUJ reshen jihar, Yakubu Mustapha Bina, na tsawon sa’o’i da dama a ofishin hukumar DSS da SCID bisa rahoton da ya rubuta kan matsalar ‘yan bindiga da kuma yada wani labari da aka ce ya sabawa wata mai mukami a gwamnatin jihar.
Amnesty International, Kungiyoyi da Jama’a Sun Yi Alla-wadai
Kungiyar Amnesty International da wasu kungiyoyin fararen hula ciki har da Accountability Ambassadors da ke Minna, sun yi Allah-wadai da matakin gwamnan.
Amnesty International ta bayyana cewa matakin ya nuna yunkurin murkushe ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma barazana ga ’yancin aikin jarida.
“Gwamna Bago bai da ikon rufe gidan rediyo a karkashin doka. Zargin da ya yi na zuga tashin hankali ya nuna rashin iya tafiyar da mulki. Dole ne ya janye umarnin nan da nan,” inji kungiyar.
Kungiyar Accountability Ambassadors ta bayyana cewa rufe gidan rediyo ba tare da bin doka ba na da illa ga kundin tsarin mulki da kuma dimokuradiyya.
“Sashe na 39 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya ba kowa ‘yancin fadin albarkacin baki da samun bayanai ba tare da tsangwama ba. Rufe gidan rediyo ba tare da izinin NBC ba, na nuni da danniya da rashin juriya ga suka,” inji shugaban kungiyar, Muhammad Alfa Muhammad.
Wani hadimin gwamnan, Yahaya Adam Idrees, a shafinsa na Facebook ya bukaci a sake nazarin umarnin gwamnan domin bai dace
Source: Daily Trust
