Kudin Fansa: Yan Bindiga Suna karɓar Zinari a Matsayin kuɗin a Zamfara

Lawan Dare, Gwamnan Zamfara

Garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa ba sabon abu ba ne a arewa maso yammacin Najeriya, sai dai a lokuta daban-daban ƴan fashin kan sauya salon ayyukan nasu domin yin ɓadda-bami ko sajewa da yanayi.

Sau da yawa sukan daɗe suna amfani da wani salo kafin bayani ya fito fili saboda yadda suke gudanar da ayyukan nasu a cikin ƙauyuka, da kuma barazanar da sukan yi wa al’umma.

A bisa yadda aka saba a arewa maso yamma, masu garkuwar kan karɓi kuɗaɗe, babura da kuma kayan abinci daga dangin waɗanda suke garkuwa da su kafin su sako su.

Sai dai wani sabon bayani da ya ɓulla a yanzu shi ne yadda suka koma karɓar zinari a matsayin kuɗin fansa ko kuma a matsayin harajin da sukan ƙaƙaba wa mazauna ƙauyuka.

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Zamfara Circle Community Initiative ta yi zargin cewa a yanzu ƴan bindgar suna sanya wa ƙauyuka harajin zinari.