Hukumar Hakkin Mallaka ta Najeriya (NCC) ta samu nasarar rufe gidan yanar gizo moviebox.ng, wani shafin intanet da ake zargi da aikata laifin keta hakkin mallaka a cikin yanar gizo.
Rufewar shafin ta fara aiki ne tun daga ranar 20 ga Yuli, tare da hadin gwiwar Nigeria Internet Registration Association (NiRA), wadda ke da alhakin rijistar sunayen shafukan yanar gizo masu .ng a Najeriya.
Shugaban hukumar NCC, Dr. John Asein, ne ya bayyana hakan, inda ya ce ayyukan haramtattun da shafin moviebox.ng ke gudanarwa na nuna wani tsari ne na kokarin ci gaba da aikata fashi da makami ta hanyar yanar gizo (piracy) ta amfani da shafuka masu kama da juna ko madadin shafuka.
Ya kara da cewa shafin yana amfani da dabaru masu zurfi don kauce wa gano shi da kuma dakatar da shi, ta hanyar girkawa da amfani da madadin shafuka (mirror domains) da ke bayar da dama ga fina-finai da sauran abun da aka killace hakkin mallakarsu.
Asein ya gargadi jama’a da su guji amfani da shafukan da ke yin alkawarin kallon fina-finai kyauta ko sauke su ba tare da biyan kudi ba, yana mai cewa ba wai kawai suna keta dokar hakkin mallaka ba ne, har ma suna jefa masu amfani da su cikin hadurran muggan cututtuka ta intanet, kamar malware, zamba ta yanar gizo, satar bayanan mutum, da aikata damfara.
Hukumar NCC ta jinjinawa NiRA bisa saurin martani da hadin kai da ta bayar, kuma ta bukaci sauran masu ruwa da tsaki a fannin intanet – musamman kamfanonin bayar da sabis na intanet (ISPs) da sauran masu shiga tsakani – da su dinga daukar mataki cikin gaggawa da amana idan aka aika musu da umarnin toshewa ko gargaɗi, kamar yadda dokar Hakkin Mallaka ta 2022 ta tanada.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa tana aiki tukuru domin dakatar da sauran madadin shafukan da ke da alaka da moviebox.ng.
Kungiyoyin masu hakkin mallaka a bangarorin fina-finai, kiɗa, da watsa shirye-shirye sun yaba matakin da aka dauka, suna mai cewa hakan ci gaba ne mai kyau wajen yaki da satar fasaha ta yanar gizo.
Wannan matakin yana daya daga cikin shirye-shiryen yakin NCC da ake kira “Stand Together Against Online Piracy (STOP)”, wanda aka kaddamar tun farkon shekarar nan, domin hada kai da hukumomin gwamnati, kamfanonin sadarwa, da shugabannin masana’antu don kare dukiyar fasaha da tabbatar da amintacciyar makomar dijital a Najeriya.
