Trends

WAFCON: Gwamna Fintiri Ya Karrama Kocin Super Falcons Madugu da Gida da Naira Miliyan 50

Gwamna Fintiri tare da coming Super Falcon Justine Madugu

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya karrama Kocin tawagar mata ta Najeriya (Super Falcons), Justine Madugu, da gida mai dakuna uku da kuma kyautar kudi har Naira miliyan 50 saboda jagorantar kungiyar zuwa nasara a gasar Women’s Africa Cup of Nations (WAFCON) 2025 da aka gudanar a Maroko.

Koci Madugu, wanda dan asalin Karamar Hukumar Numan ne a Jihar Adamawa, ya samu kyakkyawan tarba a fadar gwamnati da ke Yola, inda Gwamna Fintiri ya yaba da kishinsa, hazakarsa wajen dabarun wasa, da kuma kwarewarsa a shugabanci. Ya ce Najeriya ta lashe kofin WAFCON karo na 10 – wanda ya kafa tarihi – a karkashin jagorancin Madugu.

Yayin da yake gabatar da kyaututtukan, Gwamna Fintiri ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da bunkasa harkokin wasanni a jihar, inda ya ambaci wasu muhimman ayyukan da ake gudanarwa kamar gina filayen wasa na zamani. Ya kuma bukaci Madugu da ya rika horar da sabbin ’yan wasa matasa a jihar domin gina ci gaban wasanni mai dorewa.

Madugu, cikin jin dadin wannan karamci, ya bayyana godiyarsa tare da bayyana aniyarsa na barin tarihi mai kyau a jiharsa. Ya jaddada bukatar karfafa gwiwar mata a harkar wasanni da kuma bada cikakken goyon baya ga ci gabansu.