Trends

Shugaban EFCC Ga Sabbin Mambobin Kwamitin Gudanarwa: Kar Ku Bari In Ganku Cikin Kwamarmu

Shugaban Hukumar Yaki da cin Hanci da rashawa ta Kasa Ola Olukoyede

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya gargadi sabbin shugabanni da mambobin kwamitin gudanarwa na hukumomin gwamnatin tarayya da su kasance masu gaskiya, rikon amana da kame kai a lokacin gudanar da ayyukansu.

Olukoyede ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis yayin wani shirin horar da sabbin shugabanni da mambobin hukumomin gwamnati da aka gudanar a dakin taro na Abuja Continental Hotel.

A yayin jawabin nasa mai cike da gaskiya da bayyananniyar magana, shugaban EFCC ya bayyana yadda mutane da dama suka canja yanayin mu’amala da shi bayan nadin sa a matsayin shugaban hukumar.

Ya ce: “Fiye da kashi 50% na wadanda suka taya ni murna lokacin da aka nada ni yanzu suna kau da kai idan suka gan ni. Na gaya musu tun farko kada su taya ni murna, sai dai su yi mini addu’a.”

Yayin da ya ke taya sabbin mambobin kwamitin gudanarwa murna, Olukoyede ya yi wata gargaɗi mai nuni da muhimmanci cikin dariya:

“Ina taya ku murna da gaske. Amma don Allah, bana son na ga fuskokinku a cikin kwayar mu (sel)!”

Shugaban EFCC ya jaddada cewa yaki da cin hanci ba ya tsaya ne kawai kan kama masu laifi, sai dai ya hada da hana aikata laifin tun kafin ya faru. A cewarsa, gazawar tsarin mulki na ci gaba da haifar da laifukan kudi da cin hanci, kuma hakan yana bukatar gyare-gyare da tarbiyya mai kyau.

Ya ce: “Kama masu laifi hanya ce daya kawai. Dole ne mu kirkiri hanyoyin rigakafi masu karfi, mu raya darajar mutunci da gaskiya, tare da karfafa cibiyoyin gwamnati. Har ma tsarin shari’a yana bukatar gyara cikin gaggawa.”

Olukoyede ya kara da cewa dole ne ma’aikatan gwamnati su mai da hankali kan kame kansu da duba cikin zukatansu, maimakon kullum su dora laifi ga gwamnati.

“Sau da yawa mutane na dora laifi ga gwamnati, amma dole mu fara duba kanmu. Dole ne mu gina tsarin da zai rika bincikar kowa ciki har da wadanda ke manyan mukamai, domin cin hanci na wanzuwa ne idan babu hukunci ko sa ido.”

Ya bukaci sabbin shugabannin da su dauki mukaman da aka ba su a matsayin amanar hidima ga kasa, ba wata dama ta tara dukiya ko biyayya ga siyasa.

“Idan kuka dauki wannan mukami a matsayin wata dama ta kasuwanci ko wata lada ta siyasa, to kun riga kun lalata aikin da aka dora muku. Aikin gwamnati amana ne – kuma muna kallonku.”

Jawabin shugaban EFCC ya kara daurewar gwiwa da muhimmancin horon da ake gudanarwa, wanda aka shirya domin ba sabbin shugabannin kayan aiki, ilimi da tarbiyyar shugabanci da ya dace, a karkashin tsarin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.