Amincewar ‘Yan Kasuwa ta Ragu a Watan Yuni – Binciken CBN

Amincewar ‘yan kasuwa kan yanayin harkokin kasuwanci a Najeriya ta ragu a watan Yunin 2026, sakamakon tsadar gudanar da kasuwanci da kuma matsin tattalin arziki, kamar yadda wani binciken Babban Bankin Najeriya (CBN) kan Hasashen Kasuwanci (Business Expectations Survey – BES) ya nuna.

Binciken ya bayyana cewa Ma’aunin Amincewar Kasuwanci (Business Confidence Index – BCI) ya sauka zuwa maki 7.2 a watan Yuni, daga maki 7.9 da aka samu a watan Mayu, lamarin da ke nuna raguwar kwarin gwiwar ‘yan kasuwa duk da cewa har yanzu suna da kyakkyawan fata game da makomar tattalin arzikin ƙasa.

CBN ya ce kamfanonin da ke aiki a ɓangaren kasuwanci na hukuma har yanzu suna nuna kyakkyawan fata, sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin ke aiwatarwa da kuma ƙoƙarin bunƙasa fannoni daban-daban na tattalin arziki. Bankin ya yi hasashen cewa ma’aunin amincewar kasuwanci zai iya ƙaruwa zuwa maki 17.6 a watan Yuli, 24.1 cikin watanni uku, sannan ya kai 30.9 cikin watanni shida masu zuwa.

Binciken ya nuna cewa manyan abubuwan da ke ƙarfafa gwiwar ‘yan kasuwa sun haɗa da bunƙasa tattalin arziki ta fannoni daban-daban da kashi 38.3%, da kuma matakan gwamnatin tarayya na inganta harkokin kuɗi da kashi 16.2%.

Sai dai kuma, matsalolin karancin wutar lantarki da makamashi da kashi 23.4%, tare da barazanar rikice-rikicen siyasa da tsaro a duniya da kashi 16.5%, na ci gaba da rage kwarin gwiwar masu kasuwanci.

A bangaren fannoni na tattalin arziki, fannin hakar ma’adanai da duwatsu ne ya fi nuna kyakkyawan fata, inda ya samu maki 42.9, tare da mafi girman amfani da ƙarfin samarwa da ya kai kashi 58.5%.

Bangaren noma ya inganta zuwa maki 12.2, yayin da bangaren masana’antu ya ragu zuwa maki 10.9, sannan bangaren ayyuka ya fadi ƙwarai zuwa maki 2.9.

Duk da cewa kamfanoni na sa ran samun ƙarin kasuwanci da oda a watan Yuli, binciken ya nuna cewa har yanzu suna nuna taka-tsantsan wajen ɗaukar sabbin ma’aikata.

Ma’aunin Hasashen Aikin Yi (Employment Outlook Index) ya ci gaba da kasancewa a matakin -8.3, wanda ke nuna cewa kamfanoni sun fi mayar da hankali kan rage kashe kuɗaɗe maimakon faɗaɗa yawan ma’aikata.

A bangaren yankuna kuwa, yankin Arewa maso Gabas ne ya fi nuna kyakkyawan fata da maki 29.5, sai Arewa maso Yamma da maki 19.8. Amma yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas sun nuna rashin kwarin gwiwa, inda suka samu maki -7.9 da -9.0 bi da bi, abin da ke nuna bambancin yanayin kasuwanci tsakanin sassan ƙasar.

Har ila yau, binciken ya nuna cewa samun rancen kuɗi daga bankuna na ci gaba da kasancewa mai wahala, inda ma’aunin bayar da rance ga kamfanoni masu zaman kansu ya tsaya tsakanin maki 20 zuwa 22, lamarin da ke nuna cewa tsadar kuɗin ruwa da ƙuntatawar samun rance na iya ci gaba da hana kamfanoni faɗaɗa ayyukansu a sauran watannin shekarar 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *