Trends

Kofin Duniya: Sifaniya ta Doke Faransa 2-0, ta Kai Wasan Ƙarshe

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Sifaniya ta kai wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya ta 2026 bayan ta doke Faransa da ci 2-0 a wasan kusa da na ƙarshe da aka buga a filin wasa na Dallas.

Mikel Oyarzabal da Pedro Porro ne suka zura ƙwallayen da suka bai wa Sifaniya nasarar, yayin da ‘yan wasan Faransa suka kasa karya tsaron abokan karawarsu duk da yawan ƙoƙarin da suka yi.

Sifaniya ta fara cin ƙwallo ne a minti na 22 bayan da Lucas Digne ya yi wa Lamine Yamal keta a cikin akwatin bugun fanareti, inda Oyarzabal ya zura bugun fanaretin cikin raga.

An ƙara ta biyu ne a minti na 58 bayan kyakkyawan haɗin gwiwar ‘yan wasan Sifaniya. Pedro Porro ne ya fara gina harin tun daga baya, sannan ya ci gaba da gudu ba tare da an tare shi ba kafin ya karɓi ƙwallo daga Dani Olmo, inda ya zura ta cikin raga da ƙwarewa.

Duk da cewa Faransa ta yi yunƙurin kai hare-hare tare da yin harbi sau goma zuwa raga, ta kasa samun ko da ƙwallo ɗaya.

Da wannan sakamakon, Faransa ta gaza kai wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya karo na uku a jere, a daren da kocinta Didier Deschamps ya kafa tarihin zama kocin da ya jagoranci wasanni mafi yawa a tarihin gasar.

A yanzu haka, Sifaniya ƙarƙashin jagorancin koci Luis de la Fuente za ta kara da wadda ta yi nasara tsakanin Argentina da Ingila a wasan ƙarshe da za a buga ranar 19 ga Yuli, domin neman lashe kofin duniya karo na biyu a tarihinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *