Trends

NRS: Kamfanoni Na Gaggauta Bin Tsarin e-Invoicing

Kamfanoni da ‘yan kasuwa a Najeriya na gaggauta haɗa tsarin gudanar da harkokinsu da tsarin e-Invoicing na Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (NRS), yayin da wa’adin fara bin dokar ga manyan masu biyan haraji ke ƙaratowa. Ana sa ran matsakaitan masu biyan haraji za su shiga tsarin daga baya a shekarar 2026.

Sabon tsarin ya tanadi cewa dole ne kamfanoni su aika da takardun ciniki (invoice) ta hanyar dandalin Merchant Buyer Solution (MBS), inda ake tantance kowace mu’amala tare da ba ta Lambar Shaidar Invoice (Invoice Reference Number) a matsayin tabbacin bin ƙa’ida.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a watan Fabrairu, Hukumar NRS ta yi gargaɗin cewa kamfanonin da suka kasa bin wannan tsari na iya fuskantar hukunci. Haka kuma, masu sayen kaya ko ayyuka daga irin waɗannan kamfanoni na iya rasa damar neman rangwamen VAT Input Credit.

Manajan aikin, Mohammed Bawa, ya bayyana cewa wannan shiri haɗin gwiwa ne da zai amfani kowa da kowa.

Ya ce, “Kowa zai amfana da wannan tsari—masu biyan haraji, bankuna, masu samar da fasaha, da kuma gwamnati.”

Kamfanin DigiTax Nigeria, wanda ke cikin amintattun masu samar da wannan tsarin, ya ce yana taimaka wa kamfanoni wajen haɗa tsarin ERP da na kuɗinsu da tsarin e-Invoicing na ƙasa.

Kamfanin zai kuma shirya wani taron E-Invoicing Compliance Breakfast a Legas domin tattauna jadawalin haɗa tsarin, haɗurran da ka iya tasowa, da kuma yadda masu samar da kayayyaki za su bi sabon tsari.

Bugu da ƙari, DigiTax zai fitar da wani rahoto mai taken “The State of E-Invoicing Readiness in Nigeria”, wanda zai kwatanta yadda ƙasashen Afirka ke aiwatar da e-Invoicing tare da hasashen yadda Najeriya ta shirya.

Shi ma kamfanin D’Accubin Technology, wanda ya gina tsarin fasahar e-Invoicing, ya bayyana cewa an ƙera tsarin gaba ɗaya a cikin gida domin ya dace da ƙa’idodin e-Invoicing na duniya.

Babban Daraktan kamfanin, Sadiq Arogundade, ya ce an tsara tsarin ne ta yadda zai iya faɗaɗa cikin sauƙi tare da bin ingantattun ƙa’idodin ƙasa da ƙasa.

Hukumar NRS ta kuma bayyana cewa za ta faɗaɗa tsarin zuwa matsakaitan masu biyan haraji masu samun kuɗaɗen shiga tsakanin naira biliyan 1 zuwa biliyan 5, domin ƙara yawan masu bin ƙa’idar haraji a faɗin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *