Trends

Ribar Afreximbank Ta Karu Da Kashi 25 Cikin Dari A Rubu’in Farko Na 2026

African Export-Import Bank (Afreximbank) ta sanar da karuwar ribar da ta samu da kashi 25 cikin dari a rubu’in farko na shekarar 2026, sakamakon karuwar bayar da rance, ingantaccen tsarin tafiyar da kadarori da kuma bunkasar ribar bankin.

A cikin wata sanarwa da Manajan Sadarwa Vincent Musumba ya fitar, bankin ya bayyana cewa ya kara yawan bayar da rance a lokacin, inda jimillar bashin da yake da shi ta kai dala biliyan 42, idan aka kwatanta da dala biliyan 41 a karshen shekarar 2025.

Sanarwar ta ce matsakaicin rance da aka bayar ya karu da kashi takwas cikin dari idan aka kwatanta da bara, inda ya kai dala biliyan 32, lamarin da ya taimaka wajen kara kudaden shiga daga ruwa.

Bankin ya kuma ce yana da isasshen kudaden ruwa, inda adadin kudaden da yake da su da makamantansu suka kai dala biliyan 5.6, wanda ya kai kashi 14 cikin dari na dukkan kadarorinsa.

Hakazalika, ingancin kadarorin bankin ya ci gaba da kasancewa mai kyau, inda adadin bashin da ba a biya ba ya tsaya a kashi 2.40 cikin dari, kusa da yadda yake a shekarar 2025 kuma kasa da matsakaicin masana’antar banki.

Kudaden masu hannun jari sun karu zuwa dala biliyan 8.6 daga dala biliyan 8.4 a karshen shekarar 2025, sakamakon karin jarin cikin gida da ya kai dala miliyan 268.9 da kuma sababbin zuba jari.

Kudaden shiga daga ruwa bayan cire kashe-kashe sun karu da kashi 24 cikin dari zuwa dala miliyan 510, yayin da jimillar kudaden shiga daga ruwa suka tashi da kashi 14 cikin dari zuwa dala miliyan 813.6.

Bankin ya kuma ci gaba da rike ingantaccen tsarin jarin kariya da ya kai kashi 23 cikin dari, tare da kiyaye kashe-kashen gudanarwa a kashi 19 cikin dari, wanda ya yi kasa da iyakar kashi 30 da bankin ya tsara.

Ribar da bankin ya samu a wannan lokaci ta kai dala miliyan 268.9 idan aka kwatanta da dala miliyan 215.4 a rubu’in farko na shekarar 2025.

Babban Mataimakin Shugaban Bankin, Denys Denya, ya ce sakamakon ya nuna karfin bankin duk da matsin tattalin arzikin duniya da rashin tabbas.

Ya ce, “Duk da ci gaba da rashin tabbas a duniya, karuwar barazanar siyasa da tsauraran yanayin kasuwannin kudi, kungiyar ta samu kyakkyawan sakamako a rubu’in farko.”

Denya ya kara da cewa ingantaccen tsarin tafiyar da kadarori, kyakkyawan ingancin basussuka da kuma karfin jarin kariya ne suka taimaka wajen wannan ci gaba.

Ya ce, “Karuwar kudaden shiga daga ruwa da kuma ribar da aka samu na nuna karfin tsarin gudanarwarmu da kuma muhimmancin aikin da aka dorawa bankin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *